Maguire ya janyo wa Man Utd canjaras da Sevilla a gasar Europa
Dan asalin kasar Austria, Marcel Sabitzer wanda ke buga wasan aro a Manchester United shi ya zura kwallayen biyu a raga cikin minti takwas.
Manchester United ta ga ci ta ga rashi a karawarsu da Sevilla FC, a zagayen kusa da na karshe na cin Kofin Europa.
Man U ta ci kwallaye biyu tun a minti 21 da fara wasan, amma a cikin minti takwas na karshen wasan, sai ‘yan wasanta biyu, Tyrell Malacia da Harry Maguire suka ci gida, aka tashi 2 da 2.
Wasan da aka buga a Old Trafford, wasa ne tsakanin sa’anni, duk da dai Sevilla ne kulob din da ya fi kowa a duniya cin Kofin na Europa, domin kuwa ya daga kofin har sau shida.
Su kuwa Man U, sau daya tal suka daga kofin a kakar wasa ta 2017, karkashin shugabancin Jose Mourinho.
Dan asalin kasar Austria, Marcel Sabitzer wanda ke buga wasan aro a Manchester United daga Bayern Munich shi ya zura kwallayen biyu a raga cikin minti takwas, minti 14 da minti 21 da fara wasa.
Amma kamar a mafarki, sai murnar Man U da burin kociyanta Erik ten Hag na cin kofi a gasar Turai, suka kwaranye, sakamakon kurakurai har sau biyu na ‘yan wasan Man U biyu.
Kwallon farko dan wasan Sevilla Jesus Navas ne ya doko ta, amma ta bugi bayan Malacia ta shige ragar United. Kwallo ta biyu kuwa, El Nesyri ne ya sa mata kai sai ta doki Maguire sannan ta afka ragar United.
Dan wasan baya Harry Maguire ya yi kaurin suna wajen tafka kurakurai a aikinsa na tsaron baya, wanda yakan janyo a zura kwallon a ragar kulob dinsa. Hasali ma, Kociya Ten Hag ya sha benca Maguire, inda yake maye shi da Raphael Varane.
Man U dai ta kare wasan da ‘yan wasa 10, sakamakon raunin da Martinez ya samu a mintunan karshe, bayan da Ten Hag ya riga ya kammala canjinsa.
Yayin da za a jira zango na biyu na wasan a Alhamis mai zuwa don ganin ko waye tsakanin United da Sevilla zai zarce gaba, masu sharhi kan wasanni suna ganin cewa Sevilla za ta yi nasara a karshe.