Hanyoyin kauce wa kamuwa da kansar baki da ke kashe mutum 700 duk shekara a Nijeriya
DUNIYA
5 MINTI KARATU
Hanyoyin kauce wa kamuwa da kansar baki da ke kashe mutum 700 duk shekara a NijeriyaMa’aikatar Lafiya ta Nijeriya ta tabbatar da cewa a duk shekara sama mutum 700 ke mutuwa sakamakon cutar sankarar baki a kasar.
Cutar sankarar baki wani nau’in ciwon daji ne da ke shafar sassan bakin dan adam kamar lebe da dasashi da hakori da harshe da makogwaro da cikin kumatu / Hoto: WHO Africa
18 Afrilu 2023

Daga Shamsiyya Hamza Ibrahim

Kwararru a fannin kiwon lafiya a Nijeriya sun bayyana damuwa kan yadda ake samun karuwar masu kamuwa da cutar kansar baki a kasar.

Masana harkar lafiyar sun alakanta karuwar cutar da rashin daukar kula da baki da muhimmanci da mafi yawan mutane ke yi musamman a yankunan karkara.

Hakan na zuwa ne a yayin da Ma'aikatar Lafiya ta kasar ta ce cutar kansar baki na kashe a kalla mutum 746 duk shekara a Nijeriya sakamakon rashin ziyartar cibiyoyin lafiya a kan lokaci.

A yayin da yake jawabi a taron horarwa kan hanyoyin kula da baki da Gidauniyar Cleft and facila Deformity CFDF ta gudanar a karshen makon jiya, Ministan Lafiya na Nijeriya Dakta Osagie Ehanire ya ce adadin masu kamuwa da cutar sankarar baki kan kai 1,146 a duk shekara a kasar.

Yadda ake kamuwa da ita

"Cutar sankarar baki wani nau’in ciwon daji ne da ke shafar sassan bakin dan adam kamar lebe da dasashi da hakori da harshe da makogwaro da cikin kumatu da handa da ganda da dai sauransu," a cewar Dakta Muhammad Adam na Babban Asibitin Birnin Kudu da ke jihar Jigawa a Nijeriya.

A hirarsa da TRT Afrika, Dakta Adam ya ce cutar ta fi shafar maza da kuma wadanda shekarunsu suka haura 50, sannan ta fi yawa a kasahen fararen fata.

Likitan ya bayyana wadansu abubuwa da ka iya jawo cutar kamar “sinadarin nicotin da ke cikin taba sigari ko tabar hayaki ta shisha ko kuma tabar taunawa, da shan giya da kayan maye da kuma kwayar cutar virus mai suna HPV (human papilloma virus).

"Kazalika ana gadonta daga iyaye da kakanni, da yawan shiga matsananciyar rana a kasashen fararen fata, da rashin garkuwar jiki mai karfi, duk suna cikin hanyoyin da ake kamuwa da cutar,” in ji likitan.

Dakta Razina Abbas Kwararriyar likitar kula da baki ce a cibiyar sashin kula da baki ta Jami’ar Ahmadu Bello ABU da ke Zaria, ta gaya wa TRT Afrika cewa rashin wanke baki yadda ya kamata bayan an ci abinci ma ka iya jawo cutar.

"Saboda kwayar cutar bakteriya na iya zama a cikin bakin kuma ta haifar da matsalar cutar kansa."

"Kuma ire- iren abincin da ake ci ba tare da wanke baki da sinadaren da ya kamata ba ya sa ake dada samun karuwar cutar a Nijeriya,'' a cewar Dakta Razina.

Shi ma Dakta Adam ya jaddada cewa rashin kula baki da mafi yawan mutane ke yi musamman a yankunan karkara na ta'azzara lamarin.

''Baki na daga cikin sassan jiki masu muhimmanci kuma idan ba a kula da shi ba za a iya fuskantar matsala domin yawancin cututtuka na shiga jikin dan adam ne ta baki.

Hanyoyin magance ko takaita cutar

Kwararru sun ce idan an gane ta da wuri kafin ta yadu ana warkewa.

Amma idan ta yadu yawanci nakasa mutum take har zuwa mutuwa, a cewarsu.

Akwai hanyoyin da za ka iya bi wajen kare kanka daga kamuwa da cutar in ji Dakta Muhammad Adam.

  • Daina amfani da sinadaran nicotin da ke kunshe a taba sigari da sauransu da aka ambata a baya

  • Daina shan giya da kayan maye

  • Yin rigakafin cutar HPV

  • Yawan cin kayan lambu kamar manyan lemon tsami da karas don za su taimaka wajen gyara baki

  • Wanke baki da sinadarin Floride zai taimaka wajen kashe kwayoyin cuta da ke iya cutar da baki

  • Zuwa asibiti don duba sassan cikin baki musamman bangaren likitocin baki da hakori, duk bayan wata shida ko kuma ko da sau daya a shekara

  • Yawan wayar da kan al’umma.

An ware kowane watan Afrilu na duk shekara a matsayin watan wayar da kan al’umma kan cutar sankarar baki.

An yi hakan ne don likitoci da kwararru a fannin kula da baki su dinga haduwa suna fadakar da mutane illar da ke tattare da cutar da hanyoyin magance ta, da kuma inda aka kwana game da yaki da ake yi da ita.

MAJIYA:TRT Afrika
Rumbun Labarai
Yadda amfani da magungunan antibiotic barkatai ya sa cututtuka suka zama makamai
Rundunar Sojin Ruwan Pakistan ta kama mugwayen ƙwayoyi na dala biliyan ɗaya a Tekun Arebiya
An gano sauro a karon farko a ƙasar Iceland
Yadda hukumomi a India suke farautar Musulmai da suke cewa 'Ina son Annabi Muhammad'
Putin ya gargaɗi Trump cewa bai wa Ukraine makamai mai linzamin Tomahawk zai jawo matsala tsakaninsu
Abin da muka sani game da mummunar arangamar kan iyaka tsakanin sojin Pakistan da Afganistan
Waiwayen 1903: An taɓa yi wa Yahudawa tayin Afirka, kamar yadda ake so a mayar da Falasɗinawa yanzu
An naɗa Sarah Mullally mace ta farko Shugabar Cocin Ingila
Yadda mutuwar ɓauna a turmutsutsu ke sauya salon farautar manyan namun dawa
An tsinci gawar jakadan Afirka ta Kudu a Faransa a wajen otal a birnin Paris
Babban Alkalin Kotun Amurka ya dakatar da umarnin Trump na korar ma’aikatan VOA
UNGA: Yadda ta kaya a taron 'nuna wa juna yatsa da huce haushi' na Majalisar Dinkin Duniya
Yadda jami'an diflomasiyyar duniya suka fice daga Zauren UNGA yayin da Netanyahu zai yi jawabi
Jawabin Trump a taron MDD ya fito da sakamakon nuna ƙyamar Musulunci a duniya
An yanke wa tsohon Shugaban Faransa Sarkozy hukuncin shekara biyar a gidan yari
UNGA 80: Trump ya yi alkawarin hana Isra'ila shirin ƙwace Yammacin Kogin Jordan
Ga manyan batutuwa huɗu daga jawabin Sarkin Qatar a taron UNGA
Muradun Ƙungiyar G7 a UNGA sun haɗa da ƙara tallafa wa Ukraine da neman tsagaita wuta a Gaza
UNGA 80: Ɓaramɓarama bakwai da Trump ya yi a taron MDD na New York
Amazon da Microsoft sun buƙaci ma’aikatansu su zauna a Amurka bayan bizar H-1B ta koma $100,000