Hukumar yaki da ta'addanci ta Morocco ta sanar da daƙile wasu hare-haren ta'addanci da dama da suka shafi wurare masu muhimmanci da tsaron jama'a, waɗanda ake zargin wata ƙungiya mai alaƙa da reshen Sahel na Daesh ta shirya..
An kama mutane goma da ake zargi a lokacin ayyukan da aka tsara a biranen Agadir, Taroudant, Casablanca, El Hajeb, Tetouan, Fkih Ben Salah, da Safi, a cewar wata sanarwa daga Babban Ofishin Binciken Shari'a (BCIJ).
Binciken farko ya nuna cewa wadanda ake zargin sun yi mubaya'a ga Daesh kuma sun sami umarni kai-tsaye daga reshen ƙungiyar Sahel na kai hare-haren ta'addanci a yankin Maroko.
Wannan aikin ya nuna barazanar da kungiyoyin 'yan ta'adda ke ci gaba da yi a yankin Sahel, inda 'yan ta'addan Daesh da Al-Qaeda suka ƙara ƙarfi a Burkina Faso, Mali, da Nijar.
An kwace makamai
A lokacin bincike, hukumomi sun ƙwace makamai masu kaifi, tufafin soja, takardu ɗauke da umarnin haɗa na'urorin fashewa, kayan aiki na zamani, da sinadarai masu guba, in ji BCIJ.
Masu bincike sun kuma gano wata mota da aka gyara da ake zargin an yi nufin amfani da ita a harin ƙunar baƙin wake, ko kuma harin da za a kai ta hanyar amfani da ababen hawa.
Jami'an tsaro sun ƙara gano tukunyar gas da na'urorin girki, wasu cike da kusoshi da tsarin wayoyi na lantarki, a wani rumbun ajiya da ƙungiyar ke amfani da shi.
A cewar alkaluman BCIJ, rassan Daesh na Afirka ya ɗauki mayaƙa sama da 130 a Morocco a cikin 'yan shekarun nan.
Tun lokacin da aka kafa ta a shekarar 2015, BCIJ ta ce ta wargaza tarin 'yan ta'adda kuma ta kama mutane sama da 1,000 da ake zargi da alaƙa da ƙungiyoyin ta'addanci.
Harin ta'addanci na karshe da aka rawaito a Morocco ya faru ne a shekarar 2023, lokacin da mutane uku da ke da'awar mubaya'a ga Daesh suka kashe wani jami'in 'yan sanda na Maroko a Casablanca.














