| Hausa
AFIRKA
2 MINTI KARATU
Kotu ta bai wa EFCC damar karbe gidaje 324 a Kano
A cewar EFCC, ana zargi an gina gidajen ne da “kudin da aka samu ta hanyar haramun daga hukumar Kula da 'Yan Fansho ta Jihar Kano.”
Kotu ta bai wa EFCC damar karbe gidaje 324 a Kano
EFCC ta ce an gina gidajen ne da kudaden haramun. Hoto/EFCC / Others

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Nijeriya ta'annati, EFCC, ta ce wata kotu ta ba ta dama ta karbe gidaje 324 a Jihar Kano da ake zargi an gina ta hanyar amfani da kudaden haramun.

EFCC ta bayyana haka ne a sakon da ta wallafa a soshiyal midiya ranar Laraba.

Ta ce Mai Shari'a Inyang Ekwo na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, babban birnin Nijeriya "ya bayar da umarni a karbe" gidajen kamar yadda EFCC ta bukata a wajensa.

Hukumar ta ce gidajen sun hada da guda 168 da ke Sheikh Ja’afar Mahmud Adam Bandirawo City; guda 122 da ke Sheikh Nasiru Kabara (Amana City), Kano da kuma 38 da ke Sheikh Khalifa Ishaq Rabiu City, Kano.

EFCC ta kara da cewa gidajen sun hada da masu dakuna biyar-biyar, hurdudu, uku-uku da masu biyu-biyu da sauransu.

A cewarta, ana zargi an gina gidajen ne da “kudin da aka samu ta hanyar haramun daga hukumar Kula da 'Yan Fansho ta Jihar Kano.”

MAJIYA:TRT Afrika da abokan hulda
Rumbun Labarai
Kasashe da kungiyoyin kasa da kasa na taro a Geneva don habaka kokarin samar da zaman lafiya a Sudan
Darajar kuɗin Sudan ta faɗi, inda ake canza dala ɗaya an kan fam 10,000 na ƙasar
Uganda ta musanta samun  Ebola a ƙasarta bayan wata fasinja 'yar Nijeriya ta nuna alamun cutar
Gwamnatin Nijar ta haramta fitar da man fetur da gas zuwa ƙasashen waje
Ana hasashen kuɗin da Angola za ta kashe kan tallafin fetur a 2026 zai kai dala biliyan hudu
Shugaban Masar Al-Sisi ya ce zai sauka daga mulki a 2030 ba tare da tsawaita wa'adin mulkinsa ba
Africa CDC ta ce ba a san yadda aka kashe fiye da dala miliyan 700 na kuɗin yaƙi da Ebola ba
Ya zama dole Afirka ta daina tambayar ‘me duniya za ta sayar mana’ kawai
Ghana ta ware cedi 35m don farfaɗo da gandun dajin da haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida bacta ɓata
Kenya ta ƙara farashin man fetur da kashi 6 cikin 100 sakamakon rikicin Gabas ta Tsakiya
Ghana ta kama mutum 19 kan zargin laifukan intanet tare da gano damfarar dala miliyan 8.3
Nijar ta ayyana mummunan haɗarin muhalli bayan malalar mai
Gwamnatin Nijar ta kafa kwamitin magance ƙaranci da basussuka a ɓangaren man fetur
Aljeriya ta kama ‘yan Maroko 61 bisa zargin kitsa mata zagon-ƙasa
An miƙa wa 'yan kwangila ayyukan fara gina azuzuwa 357 a jihar Dosso ta Nijar
Gwamnatin Nijar ta yi watsi da buƙatar ƙarin farashin man fetur a ƙasar
MƊD: An raba mutane miliyan huɗu da gidajensu a Burkina Faso da Mali da Nijar
Sojoji na cikin mutum 71 da aka kashe a Sudan ta Kudu bayan mummunar arangama
Faransa ta kori jami’an leƙen asirin Nijar biyu daga ƙasarta
'Yar Afirka ta Kudu Navi Pillay ta ci kyautar Nobel ta Zaman Lafiya ta shekarar 2026