| Hausa
WASANNI
2 MINTI KARATU
Real Madrid ta dauki Kofin Copa del Rey
Rodrygo ne ya zura dukkan kwallayen a minti na biyu da minti na 70, yayin da Vinicius Junior ya taimaka masa.
Real Madrid ta dauki Kofin Copa del Rey
Real Madrid na murnar lashe Kofin Copa del Rey karo na ashirin. Hoto/Getty / Others

Vinicius Junior da Rodrygo sun taka muhimmiyar rawa a wasan da Real Madrid ta Copa del Rey karon farko tun 2014.

Madrid ta lashe Kofin ne bayan ta doke Osasuna da ci 2-1 a fafatawar da suka yi a filin wasa na La Cartuja ranar Asabar da daddare.

Rodrygo ne ya zura dukkan kwallayen a minti na biyu da minti na 70, yayin da Vinicius Junior ya taimaka masa suka kai ga nasarar lashe Kofin wanda shi ne karo na ashirin a tarihin kungiyar.

Dan wasan Osasuna Lucas Torró ne ya taimaka wa kungiyarsa ta ci kwallo daya a minti na 58.

Sai dai duk da goyon bayan da suka rika samu daga magoya bayansu 25,000 don ganin sun dauki wani babban Kofi a karon farko a tarihinsu na shekara 103, ba su yi nasara ba.

MAJIYA:TRT World