| Hausa
DUNIYA
2 MINTI KARATU
Saudiyya ta ki yin sulhu da Isra'ila sai an bai wa Falasdinawa 'yanci
"Idan ba a sama wa Falasdinawa zaman lafiya ba, idan ba a magance matsalolin da suke fama da su ba, duk wata kyautata alaka tana da iyaka," in ji Yarima Farhan.
Saudiyya ta ki yin sulhu da Isra'ila sai an bai wa Falasdinawa 'yanci
Yarima Farhan ya gaya wa Antony Blinken cewa Saudiyya tana yin abin da ta ga ya dace ne ba domin an tursasa mata ba. Hoto/  Saudi Gazette / Others

Saudiyya ta ce yana da muhimmanci ta kyautata dangantaka da Isra'ila mai makwabtaka "saboda ci-gaban yankin" amma hakan ba zai yiwu ba sai an tabbatar da "martaba da adalci" ga Falasdinawa.

Ministan Harkoki Wajen Saudiyya Yarima Faisal bin Farhan ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai da Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken wanda ke ziyara a kasar.

"Idan ba a sama wa Falasdinawa zaman lafiya ba, idan ba a magance matsalolin da suke fama da su ba, duk wata kyautata alaka tana da iyaka," in ji shi.

Yarima Farhan ya bai wa Amurka shawarar mayar da hankali wajen ganin an samu kasashe biyu - Isra'ila da Falasdinu - domin kuwa hakan ne zai zama adalci ga Falasdinawa.

Ya gaya wa Antony Blinken cewa Saudiyya tana yin abin da ta ga ya dace ne ba domin an tursasa mata ba.

“Idan ka ga mun yi wani abu, mun yi shi ne don radin kanmu kuma ba na tsammanin matsa lamba a kanmu zai taimaka,” in ji Yarima Farhan.

A gefe guda, Blinken ya yi kira ga Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da kada ya yi kafar-ungulu a shirin samar da kasashe biyu - Isra'ila da Falasdinu - jim kadan bayan ya gama tattaunawa da Yarima Farhan.

Blinken ya yi magana ta wayar tarho da Netanyahu domin tattaunawa kan "kyautata dangantakar Isra'ila da Gabas ta Tsakiya ta hanyar inganta zaman lafiya da kasashen yankin," a cewar kakakin Ma'aikatar Wajen kasar Matthew Miller.

MAJIYA:TRT Afrika da abokan hulda
Rumbun Labarai
Trump ya ce Qatar ta yi tayin ba shi kyautar jirgin sama samfurin 747 bayan ya nemi a ba shi aro
Gwamnatin Trump na binciken Ilhan Omar, za ta ƙwace takardarta ta ‘yar ƙasa tare da korar ta: Rahoto
An cire wani sashe na huhun Fafaroma Leo bayan yi masa tiyatar kansa - Fadar Batikan
Koriya ta Arewa ta 'harba makamai masu linzami da dama cikin tekun Japan'
Trump ya ce rashin ba shi kyautar Nobel ta Zaman Lafiya 'abin kunya ne'
Faransa ta ce za ta bai wa Saudiyya kariya a ɓangaren man fetur ɗinta
HRW: Tasa ƙeyar ’yan Ci-rani zuwa Afirka da Amurka ke yi azabtarwa ce
Trump na shirin kai wa Iran hari kafin zaɓen tsakiyar wa'adi a Amurka - rahoto
WHO ta yi kira ga Rasha da ta yi gaskiya game da rahotannin mutuwa sakamakon annobar ciwon huhu
Amurka ta janye dukka jiragen yaƙinta na B-1 daga sansanin sojin saman Birtaniya saboda tsoron hari
Trump ya yi gargaɗin cewa yaƙi da Iran zai zo ƙarshe ko ta halin ƙaƙa 'nan ba da jimawa ba’
An ceto baƙin-haure 260 a gaɓar tekun Mauritania
Sau takwas sojojin Amurka na yunƙurin kashe kansu a cikin USS Abraham Lincoln, in ji gwamnatin Trump
Kwamitin Zaman Lafiya na Duniya zai gabatar da shirin farfado da Gaza na dala biliyan $2.45: Rahoto
Erdogan a UNGA: Gaza ce sansanin tsare mutane mafi muni da rashin tausayi da abin kunya a zamaninmu
Trump ya yi wa Iran barazana, ya kira ICC ‘marar gaskiya‘, ya sauya sunan AI zuwa ‘SI’
Amurka ta kai 'yan ci-rani fiye da 25,000 da ta kora zuwa ƙasashen da ba su da alaƙa da su: Bincike
Antonio Guterres ya nemi a bai wa Afirka kujerun dindindin a Kwamitin Tsaro na MDD
Trump ya sa hannu kan sabuwar dokar takunkumi ga Rasha: China da India na iya fuskantar sabon haraji
Kasashen Yamma na shirin yaƙi da Rasha: Lavrov