Jami'an leken asirin Turkiyya sun 'kawar da' 'yan ta'adda a arewacin Syria
Tun 2016 Turkiyya ke kai samame arewacin Syria domin dakile ta'addanci da kuma tabbatar da tsaron mazauna yankin.
Jami’an tattara bayanan sirri na Turkiyya sun “kawar da” ‘yan ta’addan PKK/KCK-PYD/YPG 11 a arewacin Syria, kusa da iyakar Turkiyya, kamar yadda majiyoyin tsaro suka tabbatar.
A ranar Lahadi, Hukumar Leken Asiri ta Turkiyya (MIT) ta kai samame a yankin Manbij, kamar yadda majiyar wadda ta bukaci a sakaya sunanta ta bayyana.
MIT, wadda ke yawan sa ido kan maboyar ‘yan ta’adda a Manbij, ta gudanar da leken asiri mai kwari inda daga baya ta ci gaba da aiki tare da dakarun Turkiyya.
Ta lalata wani sansani mallakar kungiyoyin ta’addanci na YPG/PKK tare da kawar da ‘yan ta’dda 11, kamar yadda majiyoyin suka tabbatar.
Turkiyya da Amurka da Tarayyar Turai sun ayyana PKK a matsayin kungiyar ‘yan ta’adda – kuma ta jawo mutuwar sama da mutum 40,000 ciki har da mata da kananan yara.
Kungiyar YPG abokiyar tarayyar PKK ce ta Syria.