KASUWANCI
2 MINTI KARATU
Farashin koko ya yi tashin da bai taba yi ba a shekaru 46
Ambaliyar ruwan da ake fama da ita a wasu gonakin koko na kasar Ivory Coast na cikin abubuwan da ke haddasa karancinsa.
Farashin koko ya yi tashin da bai taba yi ba a shekaru 46
Ana samar da koko a kasashe irinsu Ivory Coast da ke Yammacin Afirka sannan a kai shi kasashen Turai don sarrafa shi wurin yin cakulet./Hoto:  REUTERS/Luc Gnago
29 Yuni 2023

Farashin koko ya yi tashin da bai taba yin irinsa ba a cikin shekara 46 a kasuwar cinikinsa da ke birnin Landan ranar Laraba.

Hakan na faruwa ne a yayin da mummunan yanayi a Yammacin Afirka yake barazana ga noman koko don kai shi kasashen da ke sarrafa shi wurin yin cakulet.

An sayar da kowanne metirik tan na koko a kan fam 2,590 ranar ta Laraba. Wannan ne karon farko da aka sayar da shi a irin wannan farashi tun 1977, shekarar da aka yi cinikin kowanne metirik tan na koko a kan fam 2,594.

Farashin koko na tashi ne sakamakon karancinsa a kasuwar hada-hadar koko ta duniya idan kasashen da ke noma shi - Ivory Coast da Ghana suka fuskanci matsala.

Bayanai sun nuna cewa an samu raguwar fitar da koko daga Ivory Coast da kashi 5 cikin dari a kakar bana.

A wannan watan hukumar da ke cinikin koko ta duniya (ICCO) ta ce za a fuskanci gibin samar da koko a fadin duniya inda zai ragu daga metirik tan 142,00 zuwa 60,000.

"Wannan ce kakar koko ta biyu a jere da ake fuskantar gibin samar da shi," a cewar Leonardo Rosseti, wani mai sharhi kan kasuwar koko ta StoneX.

Ambaliyar ruwan da ake fama da ita a wasu gonakin koko na kasar Ivory Coast na cikin abubuwan da ke haddasa karancinsa.

MAJIYA:Reuters
Rumbun Labarai
Ana hasashen mambobin OPEC+ za su ƙara yawan fetur ɗin da suke fitarwa yayin da farashinsa ke karewa
Gwamnatin ƙasar Ghana ta ƙara farashin koko
Nijar ta samu tallafin $145m daga bankin AfDB domin inganta makamashi da tattalin arziki
Elon Musk na dab da zama mutum na farko da arzikinsa ya kai tiriliyan a duniya: rahoto
Dangote zai mai da ma'aikatan Matatar Mai da aka kora daga aiki - Ma'aikatar Ƙwadagon Nijeriya
Kamfanin Orano na Faransa ya ce ya tara tan 1,500 na uranium a Nijar
Kamfanonin haɗin gwiwa ƙarƙashin Saudiyya za su sayi kamfanin wasannin game na Electronic Arts (EA)
Kamfanin Turkish Airlines zai sayi jiragen sama na Boeing 225 bayan Trump da Erdogan sun tattauna
Hukumomi a Ghana sun kama mutanen da ake zargi da yin fasa-ƙwaurin zinari
Matatar mai ta Dangote ta yi watsi da jita-jitar dakatar da aiki na wasu watanni
Babban Bankin Ghana ya dakatar da lasisin cinikin kuɗin ƙetare na UBA da wasu manhajojin aika kuɗi
Farashin ƙwallon kaɗanya ya faɗi warwas a Nijeriya bayan ƙasar ta dakatar da fitar da shi
Babban Bankin Ghana ya ba da sabbin sharuɗɗan kuɗaɗen ƙetare ga masu shiga da kayayyaki
Madogarar bincike kan abincin da aka sauya wa halitta (GMO), da dalilan karɓuwarsa a Nijeriya
Manoman koko a Ghana sun fi takwarorinsu samun farashi mai kyawu a Yammacin Afirka – COCOBOD
Nijeriya na sa ran ganin sakamako mai kyau bayan aiwatar da wani kyakkyawan tsari a harkar kamfanoni
Kamfanin Tsaro na Turkiyya zai ƙulla yarjejeniya da Malaysia don samar mata da motocin yaƙi
Turkiyya da Libya sun kulla yarjejeniyar hakar ma’adanai, samar da makamashi da ababen more rayuwa
Filin jiragen sama na Istanbul ya sake cirar tutar tashin jirage a Turai, in ji Ministan Sufuri
China da Amurka sun cim ma yarjejeniyar kasuwanci