Hukumar EFCC mai yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin Nijeriya ta’annati ta ce ta samu nasarori masu tarin yawa a shekarar 2024 ciki har da ƙwato naira biliyan 365.4 da kuma nasara kan masu laifi 4,111 a kotuna.
Wata sanarwar da hukumar ta EFCC ta wallafa shafinta na X ta bayyana cewa shugaban hukumar, Ola Olukayode, ya jinjina wa ma’aikatar hukumar domin sadaukar da kai da kuma kamun-kai da suka yi wajen cim ma nasarorin.
Olukayode, da ya bayyana wannan a wani taron kwana uku na tattauna matsaloli da makomar hukumar a birnin Uyo na jihar Akwa ibom, ya jaddada shirin hukumar na inganta aiki da ƙarewa da gaskiya wajen yaƙi da laifukan yi wa tattalin arziƙin ƙasar zagon ƙasa da kuma sauran ayyukan cin hanci da rashawa.
Shugaban na EFCC ya bayyana cewa “aiki da ƙwarewa da gaskiya muhimman ababe ne ga makoma da kuma ingancin hukumar EFCC,” in ji sanarwar.
Ɗaya daga cikin muhimman masu gabatar da jawabi a taron, Farfesa Tonnie Iredia, ya ce mugun fahimtar da aka yi wa hukumar EFCC ɗin na da nasaba ne da yadda ake murɗa labarai da gangan tare da rashin yarda.









