| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
Rundunar sojin Nijeriya ta sanya tukuicin N60m kan kwamandan ISWAP da mataimakinsa
Rundunar ta ce za ta ba da naira miliyan 50 ga duk wanda ya samar mata bayanai da za su kai ga kama kwamandan ƙungiyar ta’addanci ta ISWAP, Abu Musa Al-Mangawi Baa Shuwa.
Rundunar sojin Nijeriya ta sanya tukuicin N60m kan kwamandan ISWAP da mataimakinsa
Rundunar sojin Nijeriya ta sanya tukuicin Naira Miliyan 60 kan shugaban ISWAP da mataimakinsa da ake nema ruwa-a- jallo

Rundunar sojin Nijeriya ta sanya tukuicin Naira miliyan 60 ga duk wanda ya samar mata da bayani kan yadda za ta kama kwamandan ƙungiyar ISWAP a Yammacin Afirka da mataimakinsa da ake nemansu ruwa-a-jallo a yankin Tafkin Chadi.

Rundunar ta bayyana haka ne a wata sanarwa da muƙaddashin mai magana da yawun rundunar Operation Hadin Kai na yankin Maiduguri, Kyaftin Mohammed Goni ya fitar ranar Laraba.

Rundunar ta ce za ta ba da naira miliyan 50 ga duk wanda ya bayar da bayanai da za su kai ga kama kwamandan ƙungiyar ta’addanci ta ISWAP, Abu Musa Al-Mangawi Baa Shuwa, yayin da shi kuma mataimakinsa, Muhammad Jidda aka sanya tukuicin naira miliyan 10 ga duk wanda ya samo bayanai akansa.

Masu AlakaTRT Afrika - Dakarun Nijeriya sun kama mutanen da ake zargi da kai wa 'yan Boko Haram ƙwayoyi a Borno da Yobe

Ta ƙara da cewa tana neman bayanai kan yadda za ta kama Hamad Abu Hanifa, wani babban jami’in ƙungiyar ta ta’addanci.

Sanarwar ta ce an gano waɗanda ake nema ruwa-a-jallon ne ta hanyar binciken ƙwaƙwaf daga na'urorin leƙen asiri da aka samu a lokacin samamen da dakarun rundunar Operation Haɗin Kai suka kai kwanan nan a jihar Borno da ke yankin Arewa maso gabashin Nijeriya.

Daga cikin kayayyakin da aka ƙwato, har da kyamara da ake zargin an yi amfani da ita wajen ɗaukar bidiyoyin farfaganda, wadda ta taimaka wajen gane fuskoki da kuma wuraren da manyan jami'an ISWAP ke aiki a yankin Mangari-Metele-Dogon Chukun da ke kusa da Tafkin Chadi, a cewar sanarwar.

Rundunar sojin ta buƙaci jama'a da su samar da bayanai masu inganci da za su iya kaiwa ga kama waɗanda ake zargin, sannan ta yi alƙawarin kare sirrin waɗanda suka samar mata da bayanan.

 

 

Rumbun Labarai
An sace malamai shida da suka je taron addu’ar APC a Zamfara
Gwamnatin Nijeriya ta yi Allah wadai da kisan 'yan ƙasarta biyu a Afirka ta Kudu
FBI ta nemi haɗin kan EFCC don gudanar da bincike kan zargin karkatar da kuɗaɗen tallafin Amurka
Majalisar Dokokin Nijeriya ta dakatar da ziyarar aiki zuwa Afirka ta Kudu
Tinubu ya bai wa kowace 'yar tawagar ƙwallon kwandon Nijeriya dala dubu ɗari-ɗari
Mutum 511 sun kamu da cutar mashaƙo a Jihar Yobe a Nijeriya
Amurka ta aika sabbin kayayyakin soji Nijeriya
Zaben Nijeriya na 2027: Matakan Tinubu na rage talauci da alƙawarin Atiku na mayar da tallafin fetur
Jakadan Nijeriya ya ziyarci ’yan kasar 198 da ke gidan yari a Indiya
Mutane da dama sun mutu yayin da wasu ke asibiti bayan sun sha wani maganin gargajiya a jihar Ondo
Hukumar Shige da Fice ta Nijeriya ta kama wasu mutane da kudade da ake zargin kuɗin fansa ne
'Yansandan Nijeriya sun kama mutum biyu kan zargin kashe Danshagamu a Kano
Nijeriya ta naɗa sabon kwamandan yaƙi da ƙungiyar ta’addanci ta Boko Haram
NEMA ta karɓi ’yan Nijeriya 180 da aka mayar da su gida daga Libya
Sojojin Nijeriya sun kama wasu da ake zargin masu kai wa ’yanta’adda kayayyaki ne a Jihar Yobe
FIFA ta tura tawaga zuwa Nijeriya don gano ko gwamnati ta tsoma baki a murabus ɗin shugabannin NFF
INEC za ta ƙaddamar da na’urar bibiyar shirye-shiryen zaɓe kai-tsaye
An  kashe mutum 12, an jikkata 2 a sabon harin da Boko Haram ta kai wani ƙauye a Adamawa ta Nijeriya
‘Yanbindiga sun kashe mutum 10, sun sace 40 a wani ƙauyen Sokoto
Gwamnatin Jihar Filato a Nijeriya ta rufe makarantu saboda ɓarkewar cutar mashaƙo