| Hausa
GABAS TA TSAKIYA
2 minti karatu
Amurka na yaƙar Iran ne don kare ƙawayenta a Gabas ta Tsakiya da ƙasashen Yamma - Trump
Shugaban Amurka ya yi iƙirarin cewa Iran na iya zama barazana ga Turai da biranen Amurka a nan gaba, yayin da ya ƙara da cewa Washington na "ƙoƙari sosai a kan Iran."
Amurka na yaƙar Iran ne don kare ƙawayenta a Gabas ta Tsakiya da ƙasashen Yamma - Trump
Trump ya ce Amurka na fafatawa da Iran don kare kawayenta a yankin Gabas ta Tsakiya da Yamma

Shugaba Donald Trump ya ce Amurka na fafatawa da Iran don kare ƙawayenta a Gabas ta Tsakiya da ƙasashen Yamma daga hare-haren da ka iya tasowa.

"Muna yin hakan ne don taimaka wa Gabas ta Tsakiya. Muna yin hakan ne don taimaka wa Isra'ila. Muna yin hakan ne don taimaka wa kanmu saboda bayan sun lalata Isra'ila, wanda suka yi farin ciki da yin hakan, sai kuma su juyo kan Gabas ta Tsakiya, sannan su biyo kan Turai da kuma wasu biranenmu," in ji Trump a ranar Laraba.

Ya ce Amurka "tana aiki sosai kan Iran."

Ya bayyana waɗannan kalaman ne a daidai lokacin da wani sabon tashin hankali da ya kawo ƙarshen zaman ɗar-ɗar na tsawon wata guda da aka kwashe, ya ɓarke.

A ƙarshen makon jiya ne Amurka ta kai harin rokoki a Tsibirin Larak da ke Iran. Bayan nan kuma Tehran ta mayar da martani ta hanyar harba makamai masu linzami a Jordan da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa.

A ranar Alhamis, an ji ƙarar jiniya a Kuwait, inda rundunar tsaron sama ta ƙasar ke ta ƙoƙarin daƙile hare-haren makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuka a wani "babban harin Iran," a cewar Ma'aikatar Tsaron ƙasar ta shafinta na X.

Rikici ya daɗa ƙaruwa tun bayan da sojojin Amurka suka kai hari kan wuraren da Iran ke kai hari a wani tsibiri da ke Mashigar Hormuz a ƙarshen mako, inda suka ce Iran na shirin amfani da wuraren wajen dasa nakiyoyinta.

Iran ta mayar da martani ta hanyar harba makamai masu linzami a sansanonin Amurka da ke Jordan waɗanda aka daƙile su.

Rumbun Labarai
Rundunar sojin Yemen ta ce ta kashe 'yan Houthi 260 a hare-haren Taiz da Lahj
Mataimakin matuƙin jirgin FlyDubai ya sari matuƙin jirgi da 'gatari' a harin 'ta'addanci', in ji UAE
Amurka ta tura ƙarin sojoji 9,000 zuwa Gabas ta Tsakiya
Amurka ta tura wa Saudiyya da Qatar ƙarin na’urorin tsaron sama, Patriot don kare wuraren makamashi
Trump ya ƙi goyon bayan Netanyahu don sake tsayawa takara
Kotun Kolin Isra’ila na sauraren daukaka karar hukuncin hana ‘yantakara Larabawa shiga zabe
Jirgin FlyDubai ya yi saukar gaggawa a Saudiyya bayan da matuƙan biyu suka kaure da faɗa
Ghalibaf na Iran ya yi gargaɗin cewa babu ƙasar da za ta iya sayar da mai idan aka hana Tehran
Shin Isra’ila ta yi yunkurin kawar da tunanin wanzuwar Falasɗinu baki daya?
Iran za ta tilasta wa Amurka ficewa daga Gabas ta Tsakiya: Khamenei
Sojin ruwan Amurka takwas sun jikkata a harin makami mai linzami da Iran ta harba a Mashigar Hormuz
Erdogan: Yarjejeniyar Makka ba ta da manufa a kan Iran ko Isra’ila
Ƙungiyar yarjejeniyar tsaro ta Makka ta tattauna kan yin taron gaggawa don tallafa wa Saudiyya
Abbas ya yi gargaɗin cewa manufofin Isra’ila na barazana ga wanzuwar Falasdinu
Iran ta yi tayin sake buɗe Mashigar Hormuz cikin kwanaki bakwai idan Amurka ta sassauta matsin lamba
Birtaniya za ta bai wa Saudiyya 'kariyar' soji don daƙile hare-haren 'yan Houthi
Amurka ta ce za a dakatar da zirga-zirgar dukkan kamfanonin jiragen saman Iran a duniya daga Laraba
Qatar ta ce ana ci gaba da ƙoƙarin farfaɗo da tattaunawa tsakanin Amurka da Iran
Dalilan da suka sanya Netanyahu yunƙurin hana jam’iyyun Larabawa shiga zaɓe a Isra'ila
Yaƙin Amurka da Iran ya laƙume $150B na tattalin arzikin ƙasashen Larabawa a cikin wata guda: MDD