| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
Sojojin Nijeriya takwas sun rasu bayan motarsu ta taka nakiyar da aka dasa a kan titi
Sojojin Nijeriya takwas sun rasu bayan motar sintirinsu ta taka nakiyar da ’yanta’adda suka dasa a kusa da iyakar Nijeriya da Kamaru, kamar yadda wasu majiyoyin tsaro suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP a ranar Lahadi.
Sojojin Nijeriya takwas sun rasu bayan motarsu ta taka nakiyar da aka dasa a kan titi
Majiyoyin sun ɗora alhakin harin kan wani ɓangare da ya ɓalle daga ƙungiyar ‘yan ta’addan Boko Haram.

Wata motar sintiri ta sojojin Nijeriya ta taka nakiyar da ‘yanta’adda suka dasa a kusa da iyakar ƙasar da Kamaru, lamarin da ya yi sanadin mutuwar sojoji takwas, kamar yadda majiyoyin tsaro suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP ranar Lahadi.

Harin ya faru ne a ranar Asabar a Jihar Borno da ke arewa maso gabashin Nijeriya. A wannan rana ne babban hafsan sojojin ƙasar, Laftanar Janar Waidi Shaibu, ya kai ziyara Maiduguri, babban birnin jihar, biyo bayan wani hari da aka kai kan sansanin sojoji kwanaki kaɗan da suka gabata, wanda ya yi sanadin mutuwar sojoji 15 da wasu mambobin rundunar sa-kai masu yaƙi da ta’addanci biyar.

Majiyoyin sun ce iftila’in ya afka wa sojojin ne a yayin da suke duba ayyukan cire ciyayyi da tsirrai masu tsawo a gefen babbar hanyar da ke wajen garin Gamboru, wanda dakarun sa-kai na yaƙi da ta’addanci suke yi. A lokacin ne motarsu ta taka nakiyar, wadda ta fashe tare da kashe dukkan mutane takwas da ke cikinta.

Majiyoyin sun ɗora alhakin harin kan wani ɓangare da ya ɓalle daga ƙungiyar ‘yan ta’addan Boko Haram.

An tayar da nakiyar daga nesa

“Dukkan sojoji takwas da ke cikin motar sun mutu sakamakon fashewar,” in ji wani jami’in soja da ke yankin, yana mai cewa lamarin ya faru ne a ƙauyen Kinuba, mai tazarar kilomita 25 daga Gamboru.

Ibrahim Liman, wani mamba na rundunar sa-kai masu yaƙi da ta’addanci da ke taimaka wa sojoji, ya tabbatar da adadin waɗanda suka mutu.

“An dasa nakiyar ne a kan hanyar ƙasa mai ƙura, sannan aka tayar da ita daga nesa ta hanyar amfani da igiyar tayar da abubuwan fashewa,” in ji Liman.

Liman ya ƙara da cewa wani mamba na rundunar sa-kai da ke kula da aikin share ciyayi da dazuzzuka ya ji rauni sakamakon gutsutsuren abin fashewar da faɗa masa.