An samu bullar cutar Anthrax ta dabbobi a Nijeriya
Likitocin dabbobi sun ce an gudanar da gwaji da ya tabbatar cewa cutar ce, kuma tuni aka hana kowa shiga gonar.
Ma'aikatar Noma ta Nijeriya ta tabbatar da bullar cutar Anthrax da ake samu a jikin dabbobi a karon farko a kasar.
A wata sanarwa, Babban Likitan Dabbobi na Tarayya Dr Columba Vakuru ya ce an samu bullar cutar ne a wani gidan gona a Suleja da ke Jihar Neja.
Ya ce an fara gano cutar ne a ranar 14 ga watan Yuli a jikin wasu dabbobi da suka nuna alamunta.
Likitocin dabbobi sun ce an gudanar da gwaji wanda ya tabbatar da cewa cutar ce, kuma tuni aka hana kowa shiga gonar.
A yanzu haka gwamnatin Jihar Neja da ta tarayyar Nijeriya sun dauki matakan tabbatar da cewa an shawo kan cutar kafin ta yadu da gaggawa a kasar, in ji Gidan Talabijin na Kasa, NTA.
Gwamnatin ta kuma sanar da cewa akwai shirye-shirye da ake gudanarwa a fadin kasar na yi wa dabbobi kamar shanu da tumaki da awaki allurar rigakafin kamuwa da cutar anthrax.
Sannan za a saka ido sosai wajen ganin cutar ba ta yadu ba a gidajen gona da kasuwanni da mahauta.