| Hausa
AFIRKA
2 MINTI KARATU
Diphtheria: Cutar makarau ta bulla a wasu kananan hukumomin Kaduna
Gwamnan Kaduna Uba Sani ya umarci ma’aikatar lafiyar jihar ta yi gaggawar aikewa da tawagar kwararru domin gudanar da bincike kan lamarin da kuma daukar matakin da ya dace.
Diphtheria: Cutar makarau ta bulla a wasu kananan hukumomin Kaduna
A farkon watan nan hukumar dakile yaduwar cututtuka a Nijeriya NCDC ta tabbatar da barkewar cutar makarau a kasar inda ta ce ya zuwa lokacin mutum 80 ne suka mutu.  / Hoto: Reuters / Others

Gwamnatin Kaduna da ke arewa maso yammacin Nijeriya ta tabbatar da bullar cutar makarau a kananan hukumomin Kafanchan da Jema’a na jihar.

Ma'aikatar lafiya ta jihar ce ta ba da sanarwa hakan a ranar Alhamis 20 ga watan Yulin shekarar 2023.

Sanarwar ta ce an samu tabbaci kan bullar cutar bayan rahotannin da aka samu na mutuwar wasu yara wadanda ke zama a yankunan da lamarin ya shafa.

Kazalika wasu mazauna unguwannin Takau da Kafanchan A da Kafanchan B sun nuna alamu na kamuwa da cutar wadanda suka hada da rashin iya numfashi da kyau da zazzabi mai zafi da tari da samun raunin gaba daya da jin zafi a makogwaro da kuma kumburin wuya.

Tuni dai Gwamnan Kaduna Uba Sani ya ba da umarni ga ma’aikatar lafiya ta jihar da ta gaggauta aikewa da tawagarta domin gudanar da bincike kan lamarin da kuma daukar matakin gaggawa a wauraren da aka tabbatar da bullar cutar.

A farkon watan nan hukumar dakile yaduwar cututtuka a Nijeriya NCDC ta tabbatar da barkewar cutar makarau a kasar inda ta ce ya zuwa lokacin mutum 80 ne suka mutu.

NCDC ta ce ya zuwa ranar 30 ga watan Yuni a kalla mutum 798 ne suka kamu da cutar.

MAJIYA:TRT Afrika
Rumbun Labarai
Tiani: Dole ne Nijar ta warware matsalolin da suka daɗe suna dabaibaye ta kafin samun nasara
Majalisar Dattawan Aljeriya ta amince da buƙatar tura sojoji zuwa Nijar
Gabon ta janye takunkumin amfani da kafafen sada zumunta bayan watanni takwas
Kenya ta tabbatar da mutuwar mutum na biyu daga cutar Ebola
Ana fargabar mutane da dama suna ƙarƙashin ɓaraguzan gini mai hawa 12 da ya rushe a Kenya
Daga Nijeriya zuwa Kenya, mutane na tsawon rai amma ba tare da cikakkiyar lafiya ba
Hamshakiyar attajira ‘yar kasar Mali ta sa sarƙar zinare mai darajar dala miliyan 1.6
Ministocin makamashi na ƙasashen ECOWAS na taro kan ajiyar batura da dokokin kasuwannin lantarki
An saki wasu mata ’yan Turai biyu da aka yi garkuwa da su a Nijar bayan shafe watanni a tsare
Nijar: Hukumomi sun ɗauki matakan tsaro na gaggawa a Agadez bayan harin da ya kashe mutum 12
Kenya ta kulla yarjejeniyar $160m ta kiyaye muhalli, da goyon bayan magadan attajiran Amurka
Ghana na shirin tunkarar Ebola bayan ɓullar cutar a Kongo DRC da Kenya da Nijeriya
Kasashe da kungiyoyin kasa da kasa na taro a Geneva don habaka kokarin samar da zaman lafiya a Sudan
Darajar kuɗin Sudan ta faɗi, inda ake canza dala ɗaya an kan fam 10,000 na ƙasar
Uganda ta musanta samun  Ebola a ƙasarta bayan wata fasinja 'yar Nijeriya ta nuna alamun cutar
Gwamnatin Nijar ta haramta fitar da man fetur da gas zuwa ƙasashen waje
Ana hasashen kuɗin da Angola za ta kashe kan tallafin fetur a 2026 zai kai dala biliyan hudu
Shugaban Masar Al-Sisi ya ce zai sauka daga mulki a 2030 ba tare da tsawaita wa'adin mulkinsa ba
Africa CDC ta ce ba a san yadda aka kashe fiye da dala miliyan 700 na kuɗin yaƙi da Ebola ba
Ya zama dole Afirka ta daina tambayar ‘me duniya za ta sayar mana’ kawai