| Hausa
AFIRKA
3 MINTI KARATU
MDD ta dakatar da ayyukan jinkai a Nijar bayan juyin mulki
Mutanen da ke bukatar agaji sun karu daga miliyan daya da dubu dari tara a 2017 zuwa miliyan hudu da dubu dari uku a 2023 a Nijar, a cewar ofishin OCHA.
MDD ta dakatar da ayyukan jinkai a Nijar bayan juyin mulki
Mutane sun yi ta gudanar da zanga-zanga a Yamai da sauran birane bayan kifar da gwamnatin farar-hula da sojojin suka yi. / Photo: Reuters / Others

Ofishin Ayyukan Jinkai na Majalisar Dinkin Duniya, OCHA, ya dakatar da dukkan ayyukansa a Jamhuriyar Nijar bayan juyin mulkin da sojojin kasar suka yi.

A wata sanarwa da ofishin na OCHA ya fitar da maraicen ranar Alhamis, ya ce "Sakamakon abubuwan da ke faruwa a Nijar, mun dakatar da ayyukan jinkai da muke yi a can, inda da ma kasar ke fuskantar yanayin jinkai mai sarkakiya da ke da alaka da karuwar tashin hankali da kalubalen zamantakewa da kuma sauyin yanayi."

Fadar shugaban kasar Nijar ta tabbatar da cewa sojojin kasar wadanda suka toshe hanyoyin shiga fadar tun a ranar Laraba sun hambarar da Shugaba Mohamed Bazoum.

A yayin da yake ayyana goyon bayansa ga dakarun da suka kaddamar da juyin mulkin, shugaban rundunar sojin kasar ya ce matakin ya zama dole ne don "a hana mummunan fito-na -ito tsakanin rundunoni daban-daban."

Wani labari da za ku so ku karanta: Abu biyar da suka kamata ku sani game da Jamhuriyar Nijar

Miliyoyin mutane na bukatar abinci

Yawan mutanen da ke bukatar agaji ya karu daga miliyan 1.9 a 2017 zuwa miliyan 4,3 a 2023 a Nijar, a cewar ofishin OCHA.

Fiye da mutum 370,000 ne suka rabu da muhallansu da suka warwatsu a cikin kasar don neman mafaka, baya ga 'yan gudun hijira 250,000 da da ma suke neman mafaka a kasar - wadanda suka je daga kasashe irin su Nijeriya da Mali da kuma Burkina Faso.

Kazalika ana sa ran yawan masu tsananin bukatar abinci zai karu daga miliyan 2.5 zuwa miliyan uku a lokacin damina, daga tsakanin watan Yuni zuwa Agusta, a cewar hukumar ta MDD.

A yanzu haka MDD ta ware dala miliyan 584 don aiwatar da ayyukan agaji a kasar.

'Ba a kammala juyin mulki ba'

A gefe guda, Ministar Harkokin Wajen Faransa Catherine Colonna ta bayyana cewa masu yunkurin juyin mulki a Jamhuriyar Nijar "ba su kammala shi ba".

Ta bayyana haka ne ranar Juma'a inda ta ce shugaban Faransa Emmanuel Macron ya tattauna da Shugaba Mohamed Bazoum kuma yana cikin koshin lafiya.

Colonna ta ce tana fata masu juyin mulkin za su saurari kiran da duniya ke yi musu na su janye daga wannan ta'ada.

MAJIYA:TRT Afrika da abokan hulda
Rumbun Labarai
Tiani: Dole ne Nijar ta warware matsalolin da suka daɗe suna dabaibaye ta kafin samun nasara
Majalisar Dattawan Aljeriya ta amince da buƙatar tura sojoji zuwa Nijar
Gabon ta janye takunkumin amfani da kafafen sada zumunta bayan watanni takwas
Kenya ta tabbatar da mutuwar mutum na biyu daga cutar Ebola
Ana fargabar mutane da dama suna ƙarƙashin ɓaraguzan gini mai hawa 12 da ya rushe a Kenya
Daga Nijeriya zuwa Kenya, mutane na tsawon rai amma ba tare da cikakkiyar lafiya ba
Hamshakiyar attajira ‘yar kasar Mali ta sa sarƙar zinare mai darajar dala miliyan 1.6
Ministocin makamashi na ƙasashen ECOWAS na taro kan ajiyar batura da dokokin kasuwannin lantarki
An saki wasu mata ’yan Turai biyu da aka yi garkuwa da su a Nijar bayan shafe watanni a tsare
Nijar: Hukumomi sun ɗauki matakan tsaro na gaggawa a Agadez bayan harin da ya kashe mutum 12
Kenya ta kulla yarjejeniyar $160m ta kiyaye muhalli, da goyon bayan magadan attajiran Amurka
Ghana na shirin tunkarar Ebola bayan ɓullar cutar a Kongo DRC da Kenya da Nijeriya
Kasashe da kungiyoyin kasa da kasa na taro a Geneva don habaka kokarin samar da zaman lafiya a Sudan
Darajar kuɗin Sudan ta faɗi, inda ake canza dala ɗaya an kan fam 10,000 na ƙasar
Uganda ta musanta samun  Ebola a ƙasarta bayan wata fasinja 'yar Nijeriya ta nuna alamun cutar
Gwamnatin Nijar ta haramta fitar da man fetur da gas zuwa ƙasashen waje
Ana hasashen kuɗin da Angola za ta kashe kan tallafin fetur a 2026 zai kai dala biliyan hudu
Shugaban Masar Al-Sisi ya ce zai sauka daga mulki a 2030 ba tare da tsawaita wa'adin mulkinsa ba
Africa CDC ta ce ba a san yadda aka kashe fiye da dala miliyan 700 na kuɗin yaƙi da Ebola ba
Ya zama dole Afirka ta daina tambayar ‘me duniya za ta sayar mana’ kawai