Trump ya yi gargaɗin mayar da martanin soji idan ba a cika alƙawuran yarjejeniya da Iran ba
Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana a ranar Laraba cewa rundunonin Amurka za su ci gaba da kasancewa a cikin Iran da kewaye har sai an aiwatar da “ingantacciyar yarjejeniya” sosai.
Shugaban Amurka Donald Trump ya yi gargaɗin cewa zai yi martanin soja “mafi girma, mafi kyau, kuma mafi ƙarfi” idan ba a cika alkawuran yarjejeniya da Iran ba.
Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana a ranar Laraba cewa Amurka za ta ci gaba da kasancewa da gagarumar rundunar soja a cikin Iran da kewaye har sai an aiwatar da “ingantacciyar yarjejeniya” sosai, yana mai gargaɗin mayar da martani mai tsanani idan ba a mutunta alƙawuran ba.
A cikin wata sanarwa a dandalinsa na sada zumunta, Truth Social, Trump ya ce dukkan jiragen ruwan Amurka, na sama, da dakarun soja, tare da ƙarin harsasai da makamai, za su “ci gaba da kasancewa a wuraren da suke a ciki, da kuma kewayen Iran, har sai lokacin da aka yi cikakken biyayya ga INGANTACCIYAR YARJEJENIYA da aka cim ma.”
“Idan saboda wani dalili ba a yi hakan ba, wanda hakan abu ne mai wuyar faruwa, to ‘Harbi Zai Fara,’ mafi girma, mafi kyau, kuma mafi ƙarfi fiye da wanda kowa ya taɓa gani,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa an riga an cim ma yarjejeniya kan “rashin makaman nukiliya” tun “da daɗewa,” inda ya yi watsi da “dukkan kalaman ƙarya da ake yi akasin hakan.”
“Babu makaman nukiliya, sannan Mashigar ruwa ta Hormuz za ta kasance a buɗe kuma cikin tsaro,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa: “A halin yanzu, zaratan sojojinmu suna loda makamai kuma suna hutawa, suna jiran nasararsu ta gaba.”
Iran da Amurka sun sanar da tsagaita wuta ta tsawon makonni biyu a ranar Talata da nufin share fage ga yarjejeniyar ƙarshe don kawo ƙarshen yaƙin da Amurka da Isra’ila suka ƙaddamar a kan Iran ranar 28 ga Fabrairu, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar dubbai da jikkata wasu da dama a faɗin yankin.
Wannan sanarwar ta fito ne ƙasa da sa’o’i biyu kafin cikar wa’adin da Trump ya ɗiba wa Iran na ta buɗe Mashigar ruwa ta Hormuz da kuma amincewa da yarjejeniya, idan ba haka ba “dukan ci-gaba” zai ruguje.