| hausa
DUNIYA
3 MINTI KARATU
'Yan sanda sun kama Imran Khan bayan kotu ta yanke masa hukunci
A ranar Asabar ne wata babbar kotu a Pakistan ta yanke wa tsohon firaiministan kasar hukuncin zaman gidan yari na shekara uku kan zargin rashawa.
'Yan sanda sun kama Imran Khan bayan kotu ta yanke masa hukunci
Wannan ne karo na biyu da ake kama fitaccen dan siyasar na Pakistan a bana. AFP
5 Agusta 2023

‘Yan sanda a kasar Pakistan sun kama tsohon firaiministan kasar Imran Khan a birnin Lahore da ke gabashin kasar.

Lauyansa ne ya tabbatar da batun kamun a ranar Asabar bayan da kotu ta yanke masa hukuncin daurin shekara uku a gidan yari kan zargin sayar da kayan gwamnati ba bisa ka’ida ba.

A ranar Asabar ne kotu ta yanke masa hukunci kan wata shari’a da ta shafi boye kadara, inda ake ganin hukuncin da aka yanke masa zai iya hana shi tsayawa takarar siyasa.

“Alkali Humayun Dilawar ya sanar da cewa hannun da yake da shi a cin hanci ya tabbata,” kamar yadda kafar watsa labarai ta Pakistan ta ruwaito.

Kotun Islamabad ta bayar da takardar sammaci domin kama Khan bayan samunsa da laifi, inda ‘yan sanda a Lahore suka yi gaggawa suka dauke shi daga gidansa zuwa babbar birnin Pakistan.

Hukuncin yana da alaka da binciken da hukumar zaben kasar ta gudanar wanda ta gano cewa Khan ya sayar da kadarorin gwamnati a lokacin da yake kan mulki a matsayinsa na firaiminista daga 2018 zuwa 2022.

Khan bai halarci zaman kotun da a aka yi a Babbar Kotun Islamabad ba inda alkalin ya bayar da umarnin kama shi.

Masana shari’a na ganin samun Khan da laifi zai sa ya kasa yin takara a babban zaben kasar da za a gudanar kafin watan Nuwamba.

Jam’iyyar Khan, Pakistan Tehreek-e-Insaf (PTI) a wata sanarwa ta bayyana cewa tuni suka daukaka kara a Kotun Kolin kasar kan hukuncin da kotun gundumar kasar ta yanke.

Khan na fuskantar tuhume-tuhume sama da 150 tun bayan da aka hambarar da shi a Afrilun bara – zarge-zargen da yake cewa duk siyasa ce.

Tsohon dan wasan na kurket mai shekara 70 wanda ya koma dan siyasa, ana zarginsa da amfani da ofishinsa na firaiminista domin saye da siyar da kadarorin gwamnati da kasar ta samu kyautarsu a kasar waje wadanda kudinsu ya haura sama da dala 635,000.

MAJIYA:TRT Afrika da abokan hulda
Rumbun Labarai
An soke tashin jiragen sama fiye da 2,000 a Amurka yayin da harkokin gwamnati ke ci gaba da dagulewa
Zinarin da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ke shigarwa ƙasarta daga Sudan ya ƙaru yayin da ake yaƙi
COP30: Manyan masu gurbata muhalli na duniya ba su je taron sauyin yanayi na Brazil ba
Rasha ta ce tana sa ido kan Nijeriya bayan barazanar da Trump ya yi ta kai hari kasar
Zohran Mamdani: Matashi Musulmi na farko ya lashe zaɓen Magajin Birnin New York
Yadda amfani da magungunan antibiotic barkatai ya sa cututtuka suka zama makamai
Rundunar Sojin Ruwan Pakistan ta kama mugwayen ƙwayoyi na dala biliyan ɗaya a Tekun Arebiya
An gano sauro a karon farko a ƙasar Iceland
Yadda hukumomi a India suke farautar Musulmai da suke cewa 'Ina son Annabi Muhammad'
Putin ya gargaɗi Trump cewa bai wa Ukraine makamai mai linzamin Tomahawk zai jawo matsala tsakaninsu
Abin da muka sani game da mummunar arangamar kan iyaka tsakanin sojin Pakistan da Afganistan
Waiwayen 1903: An taɓa yi wa Yahudawa tayin Afirka, kamar yadda ake so a mayar da Falasɗinawa yanzu
An naɗa Sarah Mullally mace ta farko Shugabar Cocin Ingila
Yadda mutuwar ɓauna a turmutsutsu ke sauya salon farautar manyan namun dawa
An tsinci gawar jakadan Afirka ta Kudu a Faransa a wajen otal a birnin Paris
Babban Alkalin Kotun Amurka ya dakatar da umarnin Trump na korar ma’aikatan VOA
UNGA: Yadda ta kaya a taron 'nuna wa juna yatsa da huce haushi' na Majalisar Dinkin Duniya
Yadda jami'an diflomasiyyar duniya suka fice daga Zauren UNGA yayin da Netanyahu zai yi jawabi
Jawabin Trump a taron MDD ya fito da sakamakon nuna ƙyamar Musulunci a duniya
An yanke wa tsohon Shugaban Faransa Sarkozy hukuncin shekara biyar a gidan yari