Habasha ta miƙa buƙatar ɗaukar baƙuncin Gasar Kofin Nahiyar Afirka (AFCON) ta 2028, a hukumance, wanda zai zama karo na farko cikin sama da shekaru 50.
Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Habasha ta tabbatar da wannan neman a wani saƙo da ta wallafa a shafin X a daren Litinin.
Rabon da Habasha ta zama mai masaukin baƙi na gasar tun a shekarar 1976.
Habasha ce ƙasa ta biyu a yawan jama'a a Afirka, inda take da mutane kusan miliyan 130, kuma babban birninta shi ne hedkwatar Tarayyar Afirka (AU). Birnin Addis Ababa ne birnin mafi tudu a biranen Afirka, inda yake kimanin mita 2,300 daga matakin teku.
Tawagar ƙwallon ƙafa ta ƙasa ta Habasha na matsayi na 143 cikin 211 a jerin FIFA, kuma ranonta da buga gasar AFCON tun a 2021, lokacin da aka gudanar da gasar a Janairun 2022 a Kamaru, inda aka cire ta a matakin rukuni.
"Cikakken shiri"
Hukumar ta bayyana cewa, "Habasha ta miƙa a hukumance buƙatarta zuwa CAF don ɗaukar baƙuncin AFCON 2028. Wannan ya sake tabbatar da cikakken shirin ƙasar na karɓar babbar gasar ƙwallon ƙafa a Afirka."
Gasar AFCON ta ƙarshe ta gudana a Morocco, yayin da za a gudanar da karo na gaba na gasar shekara a ƙasashen Kenya, Uganda, da Tanzania.
Daga kuma gasar za ta sauya zuwa sabon fasali inda gasar za ta ringa gudana duk bayan shekaru huɗu, daga 2028, domin ta dace da sauran gasannin FIFA.
Mali, Nijar, da Burkina Faso sun nuna sha'awarsu ta yin haɗin-gwiwa wajen ɗaukar baƙuncin AFCON 2032, a cewar hukumomin kwallon ƙafar ƙasashen.















