Labarin mutuwar mutane 37 da ake zargin masu hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba a Jihar Neja a makon jiya ya matukar tayar da hankalin al’ummar Nijeriya.
Saboda hake ne ’yansanda suka kaddamar da bincike kan mutuwar mutanen, wadanda suka mutu yayin da suke tsare a hannun Hukumar tsaro ta farin kaya ta NSCDC a Jihar Neja.
Kazalika gwamnatin Nijeriya ta sanar da dakatar da jami’an NSCDC 20 waɗanda ake zargi suna da alaƙa da mutuwar mutanen.
Tun bayan faruwar wannan mummunan al’amari masana da masu sharhi da sauran mutane suke kiraye-kirayen kan cewa ya kama a mahukuntan kasar su dauki mataki ta yadda za a magance dimbin matsalolin da ake samu masu alaka da hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba.
Idan za a tuna a watan jiya biyo bayan mutuwar wasu mutum bakwai a Jihar Filato, Ministan Ma’adinai na Nijeriya, Dele Alake, ya gargadi masu hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba da su “daina kashe kansu” ta hanyar hakar ma’adinai a tsoffin ramukan da aka yasar kuma marasa lasisi, inda ya bayyana cewa akwai tsoffin ramukan hakar ma’adinai sama da 4,000 a Jihar Filato.
Kazalika Gwamnan Jihar Neja Mohammed Umaru Bago ya yi kira ga shugaban Nijeriya da ya yi amfani da karfin ikonsa domin hana ayyukan hakar ma’adanai a wuraren da ke fama da rikici fadin Jihar Neja.
Sai dai masana irinsu Dr Muhammad Bashir Abubakar da ke fannin karatun sociology a Jami’ar Ahmadu Bello ta Zaria suna ganin ya kamata gwamnati ta fara da tattara alkaluman duka wuraren da ake hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba.
Sannan ya ce mataki na biyu shi ne a kawo tsari a harkar hakar ma’adanai ta hanyar yi musu rijista da ba su lasisi kuma a samar da kungiyoyi ko kuma abin da a turancin Ingilishi ake kira cooperatives.
Malamin jami’ar ya ce sai gwamnati ta shata wa kungiyoyin iyaka wato kowace kungiya akwai yankin ko shiyyar da take karkashinta.
Kazalika Dr Muhammad ya ce yana da matukar muhimmanci a samar da tsaro saboda wasu daga cikin masu hakar ma’adanan suna fakewa da matsalar tsaron wajen ayyana wasu yankuna da suke da arzikin ma’adanai a matsayin nasu, alhali duka wuraren mallakin gwamnati ne.
Malamin jami’ar ya bayar da misalin yadda aka yi tsari a fannin man fetur din kasar wato yadda ake raba arzikin tsakanin gwamnatin tarayya da jihohi, to ya ce haka ya kamata a yi a fannin hakar ma’adanai.
Kazalika wani malamin jami’a kuma masani kan albarkatun kasa Geologist Dr Ishaka Shitu Al Mustapha na Jami’ar West London ya ce ya kamata gwamnati ta ayyana dokar ta-baci a fannin kuma wajibi ne idan ana so a tsaftace harkar hakar ma’adanai sai gwamnati ta yi wani sabon tsari.
Sannan ya ce akwai bukatar a tuntubi manyan kamfanin da suka yi shura ta fuskar hakar ma’adanai a duniya, don su bayar da shawarwari da dabarun zamani da za a yi amfani da su wajen gyara harkar a Nijeriya. (edited)





















