Chelsea za ta sayar da Hakim Ziyech ga Galatasaray
Hakim Ziyech na cikin 'yan wasan Morocco da suka kafa tarihin zama kasar Afirka ta farko da ta kai matakin dab da na karshe a gasar cin kofin duniya
Chelsea ta cimma yarjejeniyar sayar da Hakim Ziyech ga kungiyar Galatasaray ta kasar Turkiyya.
A halin yanzu dai ana sa ran dan wasan na Morocco, Hakim Ziyech, zai je a gwada lafiyarsa a kungiyar ta gasar Super Lig da ke birnin Santambul.
Dan wasan, mai shekara 30, ba ya cikin wadanda ake damawa da su a Stamford Bridge kuma a baya ya yi kokarin tafiya Paris St-Germain da Al Nassr da ke Saudiyya.
Ziyech ya buga wa Chelsea wasa 107 a dukkan gasanni tun lokacin da ya koma kungiyar a shekarar 2020 kan kudi fam miliyan 33.3.
Tsohon dan wasan na Ajax ya zauna a benci ne yayin da Blues suka yi nasarar lashe kofin zakarun Turai a shekarar 2021 kuma daya ne daga cikin manyan ‘yan wasa Morocco da suka kafa tarihi na kasancewa tawagar Afirka ta farko da kai matakin dab da na karshe a gasar cin Kofin Duniya da aka yi a Qatar a 2022.
Sai dai kuma ya koma cikin sauran ‘yan wasan da ba su da muhimmacin a kungiyar tun lokacin da kungiyar ta kashe kimamin fam miliyan 900 kan ‘yan wasa.
Ziyech ba ya cikin ‘yan wasan Chelsea da suka yi atisayen gabanin kakar bana a Amurka ba kuma ba ya cikin ‘yan wasan kungiyar da suka taka leda a karawar kungiyar da Liverpool inda suka yi canjaras a farkon wannan kakar.