Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya bai wa sababbin ministocin da ya nada ma'aikataun da kowannensu zai yi aiki a can.
Mai magana da yawun shugaban kasar Ajuri Ngelale ne ya shaida wa manema labarai hakan a fadar shugaban kasa a ranar Laraba.
An bai wa tsohon gwamnan Jigawa Badaru Abubakar Ma'aikatar Tsaro, sai tsohon gwamnan Jihar Zamfara Bello Matawalle a matsayin karamin ministan tsaro.
Sannan tsohon gwamnan Ribas Nyesom Wike shi aka bai wa Ma'aikatar Birnin Tarayya, Abuja.
Ga jerin kamar haka:
Babban Ministan Tsaro – Muhammad Badaru
Karamin Ministan Tsaro – Bello Matawalle
Karamin Ministan Gidaje da Bunkasar Birane – Abdullahi Gwarzo
Ministan Kasafin Kudi da Tsara Tattalin Arziki– Atiku Bagudu
Ministan Birnin Tarayya – Nyesom Wike
Karamar Ministar Birnin Tarayya – Mairiga Mahmud
Ministar Al’adu da Bunkasa Tattalin Arziki – Hannatu Musawa
Karamin Ministan Albarkatun Ruwa da Tsaftar Muhalli – Bello Goronyo
Ministan Gona da Samar da Abinci – Abubakar Kyari
Ministan Ilimi – Tahir Mamman
Ministan Harkokin Cikin Gida – Sa’idu Alkali
Ministan Harkokin Waje – Yusuf Tuggar
Ministan Lafiya da Walwalar Jama'a –Ali Pate
Ministan Harkokin 'Yan Sanda – Ibrahim Gaidam
Karamin Minsitan Tama da Karafa – U Maigari Ahmadu
Ministan Sadarwa da Kirkire-kirkire da Tattalin Arzikin Intanet - Bosun Tijani Ministan Muhalli - Ishak Salako
Ministan Kudi - Wale Edun
Ministan Harkokin Teku - Bunmi Tunji
Ministan Lantarki - Adedayo Adelabu Karamin
Ministan Lafiya da Walwalar Jama’a - Tunji Alausa
Ministan Ma’adanai - Dele Alake
Ministan Harkokin Yawon Bude Ido - Lola Ade-John
Ministan Sufuri - Adegboyega Oyetola
Ministan Masana’antu da Kasuwanci da Zuba Jari - Doris Anite
Ministan Kimiyya da Fasaha - Uche Nnaji
Karamin Ministan Kwadago da Ayyuka - Nkiruka Onyejeocha
Ministan Harkokin Mata - Uju Kennedy
Ministan Ayyuka - David Umahi
Ministan Matasa - Abubakar Momoh
Ministan Ayyukan Jin kai da Rage Talauci - Betta Edu
Karamin Ministan Iskar Gas - Ekperikpe Ekpo
Ministan Man Fetur - Heineken Lokpobiri
Ministan Wasanni - John Enoh
Karamin Ministan Ilimi - Yusuf T. Sunumu


















