DUNIYA
3 MINTI KARATU
Yevgeny Prigozhin: Shugaban Kamfanin Wagner ya mutu a hatsarin jirgi
Shugaban kamfanin sojojin haya na Wagner, Yevgeny Prigozhin ya mutu a wani hatsarin jirgi a Rasha, a cewar Hukumar Kula da Sufurin Jirage ta kasar.
Yevgeny Prigozhin: Shugaban Kamfanin Wagner ya mutu a hatsarin jirgi
Yevgeny Prigozhin ya jagoranci wani bore da bai yi nasara ba kan gwamnatin Rasha wata biyu da suka wuce. / Hoto: Reuters
23 Agusta 2023

Shugaban kamfanin sojojin haya na Wagner, Yevgeny Prigozhin, ya mutu a wani hatsarin jirgi a Rasha, a cewar Hukumar Kula da Sufurin Jirage ta kasar.

A ranar Laraba ne wani karamin jirgi ya yi hatsari a yankin Tver na birnin Moscow inda duk mutum 10 da suke ciki suka rasa rayukansu, in ji hukumar agajin gaggawa ta Rasha.

Kazalika wani shafin Telegram mai alaka da Kamfanin Wagner ya tabbatar da mutuwar Prigozhin a sanarwar da ya wallafa a shafin. Ya zargi gwamnatinn Rasha da alhakin kisan.

Shugaban Wagner Yevgeny Prigozhin na cikin jerin fasinjojin da ke cikin jirgin, a cewar rahotannin kafafen yada labaran Rasha.

Kazalika wani babban kwamandan Wagner Dmitry Utkin yana cikin jirgin.

"Wani karamin jirgi da ya tashi da birnin Moscow zuwa Saint Petersburg ya yi hatsari a kusa da kauyen Kuzhenkino a yankin Tver.

“Akwai mutum 10 a cikinsa jirgin da suka hada da ma’aikatansa uku. Bayanan farko-farko sun ce dukkan mutanen da ke cikin jirgin sun mutu,” a cewar Ma’aikatar Ayyukan Gaggawa ta kasar a sanarwar da ta saka a shafinta na Telegram.

Labarai masu alaka

Bore ga rudunar sojin Rasha

Prigozhin, mai shekara 62, ya jagoranci yin bore ga manyan dakarun sojin Rasha a tsakanin 23 da 24 ga watan Yuni, wanda Shugaba Vladimir Putin ya ce abu ne da zai iya jefa Rasha yakin basasa.

An kawo karshen boren bayan yarjejenya da kuma shawo kan Prigozhin da fadar Cremlin ta yi kan ya koma Belarus mai makotaka da Rasha. Amma an gan shi na kai komo a cikin Rasha duk da wannan yarjejeniya da aka kulla.

Prigozhin, wanda ya so kawar da Ministan Tsaro Sergei Shoigu da Valery Gerasimov, shugaban rundunar soji, a ranar Litinin ya yada wani faifan bidiyo da ke nuna yana wata kasa a Afirka.

MAJIYA:AA
Rumbun Labarai
Yadda amfani da magungunan antibiotic barkatai ya sa cututtuka suka zama makamai
Rundunar Sojin Ruwan Pakistan ta kama mugwayen ƙwayoyi na dala biliyan ɗaya a Tekun Arebiya
An gano sauro a karon farko a ƙasar Iceland
Yadda hukumomi a India suke farautar Musulmai da suke cewa 'Ina son Annabi Muhammad'
Putin ya gargaɗi Trump cewa bai wa Ukraine makamai mai linzamin Tomahawk zai jawo matsala tsakaninsu
Abin da muka sani game da mummunar arangamar kan iyaka tsakanin sojin Pakistan da Afganistan
Waiwayen 1903: An taɓa yi wa Yahudawa tayin Afirka, kamar yadda ake so a mayar da Falasɗinawa yanzu
An naɗa Sarah Mullally mace ta farko Shugabar Cocin Ingila
Yadda mutuwar ɓauna a turmutsutsu ke sauya salon farautar manyan namun dawa
An tsinci gawar jakadan Afirka ta Kudu a Faransa a wajen otal a birnin Paris
Babban Alkalin Kotun Amurka ya dakatar da umarnin Trump na korar ma’aikatan VOA
UNGA: Yadda ta kaya a taron 'nuna wa juna yatsa da huce haushi' na Majalisar Dinkin Duniya
Yadda jami'an diflomasiyyar duniya suka fice daga Zauren UNGA yayin da Netanyahu zai yi jawabi
Jawabin Trump a taron MDD ya fito da sakamakon nuna ƙyamar Musulunci a duniya
An yanke wa tsohon Shugaban Faransa Sarkozy hukuncin shekara biyar a gidan yari
UNGA 80: Trump ya yi alkawarin hana Isra'ila shirin ƙwace Yammacin Kogin Jordan
Ga manyan batutuwa huɗu daga jawabin Sarkin Qatar a taron UNGA
Muradun Ƙungiyar G7 a UNGA sun haɗa da ƙara tallafa wa Ukraine da neman tsagaita wuta a Gaza
UNGA 80: Ɓaramɓarama bakwai da Trump ya yi a taron MDD na New York
Amazon da Microsoft sun buƙaci ma’aikatansu su zauna a Amurka bayan bizar H-1B ta koma $100,000