| hausa
DUNIYA
2 MINTI KARATU
Putin ya yi jaje kan mutuwar shugaban Wagner Yevgeny Prigozhin
A wani jawabi da ya gabatar a talabijin, Putin ya ce kamfanin Wagner na sojojin haya, "ya ba da gagarumar gudunmawa ga Rasha" a yakin Ukraine.
Putin ya yi jaje kan mutuwar shugaban Wagner Yevgeny Prigozhin
A cewar Putin, Prighozin "dan kasuwa ne mai basira," wanda "ya san shi tun shekarun 1990." / Photo: AFP
24 Agusta 2023

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya yi tsokaci kan mutuwar shugaban kamfanin sojojin haya na Wagner, Yevgeny Prigozhin, wanda tsohon mai dafa masa abinci ne.

A wani jawabi da ya gabatar a talabijin, Putin ya ce kamfanin Wagner "ya ba da gagarumar gudunmawa ga Rasha" a Ukraine.

Shugaban kasar ya kara da cewa Rasha za ta yi bincike kan lamarin da ya jawo hatsarin jirgin da a cikinsa Prigozhin ya rasa ransa, tare da mutum tara a Rasha a ranar Laraba.

Putin ya mika sakon ta'azziyarsa ga iyalan mutanen da suka mutu a hatsarin da ya faru a yankin Tver, mai nisan kilomita 200 daga birnin Moscow a arewa maso yamma.

A cewar Putin, Prighozin "dan kasuwa ne mai basira," wanda "ya san shi tun shekarun 1990."

Putin ya ci gaba da cewa Prigozhin mutum ne da ya dinga "haduwa da kaddarar rayuwa wanda kuma ya aikata kura-kurai a rayuwarsa."

Labari mai alaka:

MAJIYA:TRT Afrika da abokan hulda
Rumbun Labarai
Zinarin da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ke shigarwa ƙasarta daga Sudan ya ƙaru yayin da ake yaƙi
COP30: Manyan masu gurbata muhalli na duniya ba su je taron sauyin yanayi na Brazil ba
Rasha ta ce tana sa ido kan Nijeriya bayan barazanar da Trump ya yi ta kai hari kasar
Zohran Mamdani: Matashi Musulmi na farko ya lashe zaɓen Magajin Birnin New York
Yadda amfani da magungunan antibiotic barkatai ya sa cututtuka suka zama makamai
Rundunar Sojin Ruwan Pakistan ta kama mugwayen ƙwayoyi na dala biliyan ɗaya a Tekun Arebiya
An gano sauro a karon farko a ƙasar Iceland
Yadda hukumomi a India suke farautar Musulmai da suke cewa 'Ina son Annabi Muhammad'
Putin ya gargaɗi Trump cewa bai wa Ukraine makamai mai linzamin Tomahawk zai jawo matsala tsakaninsu
Abin da muka sani game da mummunar arangamar kan iyaka tsakanin sojin Pakistan da Afganistan
Waiwayen 1903: An taɓa yi wa Yahudawa tayin Afirka, kamar yadda ake so a mayar da Falasɗinawa yanzu
An naɗa Sarah Mullally mace ta farko Shugabar Cocin Ingila
Yadda mutuwar ɓauna a turmutsutsu ke sauya salon farautar manyan namun dawa
An tsinci gawar jakadan Afirka ta Kudu a Faransa a wajen otal a birnin Paris
Babban Alkalin Kotun Amurka ya dakatar da umarnin Trump na korar ma’aikatan VOA
UNGA: Yadda ta kaya a taron 'nuna wa juna yatsa da huce haushi' na Majalisar Dinkin Duniya
Yadda jami'an diflomasiyyar duniya suka fice daga Zauren UNGA yayin da Netanyahu zai yi jawabi
Jawabin Trump a taron MDD ya fito da sakamakon nuna ƙyamar Musulunci a duniya
An yanke wa tsohon Shugaban Faransa Sarkozy hukuncin shekara biyar a gidan yari
UNGA 80: Trump ya yi alkawarin hana Isra'ila shirin ƙwace Yammacin Kogin Jordan