| Hausa
AFIRKA
3 MINTI KARATU
‘Yan sandan Bauchi da Kano sun yi magana kan zargin masu 'shan jini'
A 'yan kwanakin nan, ana ta yada wasu labarai a shafukan sada zumunta wadanda aka yi zargin cewa wasu masu 'shan jini' suna shiga gidajen mutane.
‘Yan sandan Bauchi da Kano sun yi magana kan zargin masu 'shan jini'
'Yan sandan Bauchi sun ce babu kamshin gaskiya cikin labarin da ake yadawa cewa masu shan jini sun shiga jihar. Hoto/Getty Images / Others

Rundunar 'yan sandan Bauchi da ke arewa maso gabashin Nijeriya ta karyata labaran da ake yadawa cewa wasu mata na shiga gidajen jama’a suna shan jininsu.

Ita ma takwararta ta jihar Kano ta yi magana a kan batun amma ta ce tana gudanar da bincike.

A tattaunawarsa da TRT Afrika, kakakin ‘yan sandan Jihar Bauchi SP Ahmed Mohammed Wakil ya karyata rahotannin da ake yadawa a soshiyal midiya cewa wasu mutum 20 da ake zargi da maita sun shiga Bauchi kuma suna shan jinin jama'a.

Ya bayar da misali da wata mata da bidiyonta ya karade shafukan sada zumunta wadda aka yi zargin tana maita, yana mai cewa ba haka lamarin yake ba.

“Matar mai suna Siddika, mazauniyar Unguwar Shekal ce, ta je wata unguwa mai suna Bakin Kura a cikin garin Bauchi domin neman sadaka, sai ta fadi saboda yunwa.

“Sai wasu mata da matasa suka fara jifanta da duwatsu, suna mai cewa mayya ce,” in ji SP Wakil.

Ya bayyana cewa bayan sun samu wannan labarin sai Kwamishinan ‘yan sandan Bauchi CP Auwwal Musa Mohammad ya bayar da umarni aka yi gaggawar ceto matar.

“Binciken da muka yi ya nuna matar tana da tabin-hankali amma ba mayya ba ce kuma mun mika ta hannun iyalanta,” in ji shi.

SP Wakil ya bukaci jama’a su daina yada jita-jita ko abin da ba su tabbatar da sahihancinsa ba.

Bincike

A Jihar Kano ma, an samu makamancin wannan lamarin inda wani bidiyo ke yawo da ke nuna ana dukan wasu mata kan zargin cewa ‘yan shan jini ne.

Haka ma akwai wasu hotuna da ake yadawa na wata mata wadda aka kama a Karamar Hukumar Gezawa wadda aka yi zargin ta sha jinin matar gidan.

TRT Afrika ta tuntubi mai maan da yawun rundunar 'yan sandan jihar ta Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa, kan wanna batu.

Duk da dai bai tabbatar ko karyata faruwar lamarin ba, ya shaida mana cewa suna gudanar da bincike.

Da muka nemi karin bayani kan ko an kai musu rahotannin faruwar irin wannan batu, sai ya ce "muna gudanar da bincike" kawai.

MAJIYA:TRT Afrika
Rumbun Labarai
Ghana ta kama mutum 19 kan zargin laifukan intanet tare da gano damfarar dala miliyan 8.3
Nijar ta ayyana mummunan haɗarin muhalli bayan malalar mai
Gwamnatin Nijar ta kafa kwamitin magance ƙaranci da basussuka a ɓangaren man fetur
Aljeriya ta kama ‘yan Maroko 61 bisa zargin kitsa mata zagon-ƙasa
An miƙa wa 'yan kwangila ayyukan fara gina azuzuwa 357 a jihar Dosso ta Nijar
Gwamnatin Nijar ta yi watsi da buƙatar ƙarin farashin man fetur a ƙasar
MƊD: An raba mutane miliyan huɗu da gidajensu a Burkina Faso da Mali da Nijar
Sojoji na cikin mutum 71 da aka kashe a Sudan ta Kudu bayan mummunar arangama
Faransa ta kori jami’an leƙen asirin Nijar biyu daga ƙasarta
'Yar Afirka ta Kudu Navi Pillay ta ci kyautar Nobel ta Zaman Lafiya ta shekarar 2026
Rikicin wakilci a yanki: Me ke ta'azzara rikicin Ethiopia-Eritrea?
Haɗuran mota sun yi sanadin mutuwar mutum 2,151 a Ghana cikin watanni tara - Rahoton MTTD
Ethiopia ta nemi a janye dakarun Eritrea 'nan-take' daga ƙasarta
Ghana da FBI sun kama mutum 130 da ke da alaƙa da zambar $10m
Babban kwamanda a mayaƙan RSF ya koma rundunar sojin Sudan tare da mayaƙa 300
Burkina Faso za ta sauya darussan makarantu don 'kawar da tsarin mulkin mallaka' a fannin ilimi
Ghana za ta nemi shiga ƙungiyar BRICS
Gambia ta sayi manyan injinan samar da wutar lantarki  biyu domin magance matsalar wuta a ƙasar
Shugaban Masar ya soki tsoma bakin ƙasashen waje a harkokin Afirka
Ƙungiyar Tarayyar Afirka ta musanta ɗora wa Masar laifin rikin Ethiopia bayan ƙin yardar Alƙahira