| Hausa
DUNIYA
4 MINTI KARATU
Sojojin Nijar sun yi garkuwa da jakadan Faransa: Emmanuel Macron
Shugabannin mulkin sojan Nijar sun shaida wa Jakadan Faransa Sylvain Itte cewa ya bar kasar tun bayan da suka hambarar da Shugaba Mohamed Bazoum ranar 26 ga watan Yuli.
Sojojin Nijar sun yi garkuwa da jakadan Faransa: Emmanuel Macron
Macron ya shaida wa manema labarai a ranar Juma'a cewa jakadan kasar a yanzu yana dogara ne a kan "abin da sojojin suke ba shi." Hoto: Reuters / Reuters
15 Satumba 2023

Shugaba Emmanuel Macron ya ce sojojin da ke mulki a Jamhuriyar Nijar sun yi garkuwa da jakadan Faransa a ofishin jakadancin kasar, tare da zargin sojojin da toshe hanyar kai kayan abinci ga ofishin.

Macron ya shaida wa manema labarai a ranar Juma'a cewa jakadan kasar a yanzu yana dogara ne a kan "abin da sojojin suke ba shi."

"A yanzu da muke maganar nan, akwai jakadanmu da kuma wani jami'in diflomasiyya da suke tsare a ofishin jakadancin Faransa," in ji shi.

"Sun hana a kai kayan abincin," ya ce, yana mai magana a kan shugabannin sojin Nijar din. "A yanzu abincin da suka ba shi yake ci."

Shugabannin mulkin sojan Nijar sun shaida wa Jakadan Faransa Sylvain Itte cewa ya bar kasar tun bayan da suka hambarar da Shugaba Mohamed Bazoum ranar 26 ga watan Yuli.

Amma har wani wa'adi na awa 48 da aka ba shi na ficewar ya wuce, bai bar kasar ba, saboda gwamnatin Faransa ta ki bin umarnin don ta ki amincewa da gwamnati mulkin sojan a matsayin halastacciya.

Faransa da mafi yawan makwabtan Nijar sun yi Allah wadai da juyin mulkin.

Macron ya ce jakadan "ba zai iya fita ba, saboda an nuna ba a son sa kuma ana hana shi abinci."

'Tsokana'

Da aka tambaye shi ko Faransa za ta duba yiwuwar mayar da jakadan gida, sai Macron ya ce: “Zan yi duk wani abu da muka amince da shi ni da Shugaba Bazoum saboda shi ne halastaccen shugaban kasa kuma ina magana da shi a kullum.”

Faransa ta jibge sojoji kusan 1,500 a Nijar, kuma a farkon watan nan ta ce za ta tattauna duk wani batun janye su ne da Bazoum.

Sabbin shugabannin kasar sun yi watsi da duk wasu yarjejeniyoyin hadin kai na soji da Faransa tare da umartar dakarunta su fice ba tare da bata lokaci ba.

An shafe makonni Macron yana yin watsi dsa kira kan kawar da jakadan Faransa, wani mataki da Kungiyar Tarayyar turai ke goyon bayansa da aka bayyana a matsayin bukata ta “neman tsokana.”

Kamar Faransa, in ji mai magana da yawun harkokin wajen EU Nabila Massrali a watan da ya gabata, EU ma ba ta dauki hukumomin da suka kwace mulki a Nijar a "matsayin halastattu ba."

Yankin Sahel da ke kusa da Sahara ya sha fama da abin da Macron ya kira annobar juyin mulki a ‘yan shekarun nan, inda gwamnatocin soji suka hambarar da zababbu na farar hula a kasashen Mali da Burkina Faso da Guinea da kuma Nijar.

MAJIYA:TRT Afrika
Rumbun Labarai
Masana kimiyya sun gano zanen shacin hannu 'mai shekara 67,800' a wani kogo a Indonesia
Ministan Wajen Saudiyya da takwarorinsa na Iran, Oman da Qatar sun tattauna kan zaman lafiyar yanki
Amurka ta dakatar da ba da bizar masu ƙaura ga 'yan Nijeriya da wasu ƙasashe 74
Wani sanatan Amurka ya yi gargaɗi kan ƙaruwar ƙyamar Musulunci da ƙin jinin Larabawa
Trump ya saka harajin kashi 25 kan ƙasashen da ke kasuwanci da Iran
An katse intanet da wayoyin hannu a Iran
Matar shugaban Turkiyya ta gana da shugaban UNRWA kan shirin buɗe ofis a Ankara
Sanatocin Republican 5 sun bi sahun 'yan Democrat don neman sake duba ikon yaki na Trump a Venezuela
An kashe ɗansanda a kusa da Tehran yayin da zanga-zanga kan matsin rayuwa ta mamaye ƙasar Iran
Erdogan da Anwar na son ƙarfafa alaƙar Turkiyya da Malaysia tare da fifita fannin tsaro
Trump ya sanya hannu kan takardar neman cire Amurka daga ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa da na MDD
Shugaban Rundunar Sojin Iran ya yi barazanar mayar da martani ga Trump da Netanyahu
Abin da ya sa ya kamata Afirka ta damu kan samamen da Amurka ta kai Venezuela
An sayar da kifi mai nauyin kilogiram 240 a kan Naira biliyan 4.5 ($3.2m) a Japan
Me zai faru ga takunkuman da Amurka ta sanya wa Venezuela bayan ta ɗauke Maduro
Tarayyar Afirka ta nuna 'damuwa', Afirka ta Kudu ta nemi a yi taron MDD da gaggawa kan Venezuela
Trump ya gargaɗi Colombia, ya nufi Cuba bayan ya kama Maduro
Amurka ba za ta bari kowa ya ci gaba daga inda Maduro ya tsaya ba - Trump
Martanin duniya na karuwa kan hare-haren da Amurka ta kai wa Venezuela
An fitar da Shugaba Maduro da matarsa daga Venezuela, in ji Trump