An gano aƙalla gawawwaki 170 a manyan ƙaburbura a gabashin Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo

Hukumomi sun sanar da gano wasu manyan ƙaburbura a gabashin Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo, a wani wurin da ƙungiyar 'yantawayen M23 ta bari kwanan bayan.

By
Gano manyan ƙaburburan a gabashin DRC ya sa ana zargin 'yantawayen M23 da kisan kiyashi / Reuters

Hukumomi da wata ƙungiyar kare hakkin bil’adama sun ce an gano manyan ƙaburbura ɗauke da gawarwaki 170 a gabashin Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo a wani wuri da kwanan baya ƙungiyar ‘yantawaye ta M23 ta bari.

Gwamnan lardin South Kivu, Jacques Purusi, ya ce an gano manyan ƙarburbura biyu a unguwannin Kiromoni da Kavimvira a wajen birnin birnin gabashi na Uvira.

"A wannan matakin, mun gano wurare biyu: wani babban kabari ɗauke da kimanin gawarwaki 30 a Kiromoni, kusa da kan iyakar Burundi a ɓangaren Kongo, ɗaya kuma a Kavimvira inda aka gano gawarwaki 141," kamar yadda Purusi ya shaida wa kamfanin dillancin labaran The Associated Press.

Shugaban ƙungiyar fafatuka ta Local Network for the Protection of Civilians, ya ce ƙungiyar ta nemi zuwa wuraren, amma sojin Kongo sun hana ta.

Bayanan da aka tattara kawo yanzu dai sun nuna cewa ‘yantawayen M23 ne suka kashe waɗanda lamarin ya rutsa da, a cewar Yves Ramadhani, mataimakin shugaban ƙungiyar.

Gwamnan da ƙungiyar fafatukar sun yi zargin cewa ‘yantawayen sun kashe mutanen ne domin suna tunanin cewa sojojin Kongo ne ko kuma mayaƙan da ke goyon bayan gwamnati.

Yaƙi a gabashin Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Kongo ya yi ƙamari a cikin ‘yan watannin nan duk da yarjejeniyar zaman lafiyar da Amurka ta jagoranci ƙullawa domin rage tashin hankali a yankin.

Sojin Kongo da ƙungiyar ‘yantawayen M23 sun fuskanci zarge-zarge daga ƙungiyoyin kare hakkin bil’adama game da kisan gilla da sauran na’uka na cin zarafi.

Gani manyan ƙaburburan na zuwa ne yayin da rikici ke ci gaba da raba fararen hula da muhallansu tare da zurfafa rashin tsaro a gabashin Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo, inda ƙungiyoyin ‘yanbindiga suka shafe shekaru suna aika-aika.