| Hausa
TURKIYYA
2 minti karatu
Turkiyya ta kama jami'an Mossad na Isra'ila biyu a Istanbul kan leƙen asiri
Hukumar Leƙen Asirin Turkiyya ta ce ta gano tare da kama wasu jami’an leƙen asirin Isra’ila waɗanda suke bai wa Isra’ila muhimman bayanai inda suka rinƙa amfani da kasuwanci domin gudanar da ayyukansu a ɓoye.
Turkiyya ta kama jami'an Mossad na Isra'ila biyu a Istanbul kan leƙen asiri
An kama mutanen ne bayan wani aiki mai sarkakiya na yaƙi da leƙen asiri da aka sanya wa suna “MONITUM.” / AA
7 Fabrairu 2026

Hukumar leƙen asirin Turkiyya (MIT) ta kama mutane biyu da ake zargi da yin aiki ga hukumar leƙen asirin Isra’ila ta Mossad, bayan wani aiki mai sarkakiya na yaƙi da leƙen asiri da aka sanya wa suna “MONITUM.”

Majiyoyin tsaron Turkiyya a ranar Juma’a sun sanar da cewa an kama Mehmet Budak Derya da Veysel Kerimoglu a wasu ayyuka na haɗin gwiwa da MIT da kuma ofishin Babban Mai Shigar da Ƙara na Istanbul da kuma sashen yaƙi da ta’addanci na rundunar ‘yansandan Istanbul suka jagoranta.

A cewar masu bincike, Derya, wanda injiniyan hakar ma’adanai ne, ya kafa wani kamfani a shekarar 2005 sannan ya buɗe wurin haƙar dutse a yankin Silifke na birnin Mersin kafin ya faɗaɗa kasuwancinsa zuwa cinikayyar ƙasa da ƙasa. Ana zargin cewa faɗaɗar hulɗar kasuwancinsa da ƙasashe da dama ta ja hankalin leƙen asirin Isra’ila.

A watan Satumban 2012, wani mutum mai amfani da sunan ɓoye “Ali Ahmed Yassin,” wanda ke aiki a madadin wani kamfani na bogi da Isra’ila ta kafa, ya ziyarci ofishin Derya tare da ba shi tayin haɗin gwiwa, a cewar majiyoyin.

Zuwa watan Janairun 2013, an gabatar da Derya ga jami’an Mossad yayin wani taro a Turai.

Gudanar da tattaunawa a wasu ƙasashe

A lokacin waɗannan hulɗoɗi, wani jami’in Mossad mai amfani da sunan ɓoye “Luis” ya nemi a ɗauki Kerimoglu, ɗan ƙasar Turkiyya wanda ɗan asalin Falasɗin ne aiki. Ana zargin cewa an umarci mutanen biyu su riƙa bayar da rahoto a tare game da dukkan ayyuka da hulɗoɗinsu.

Majiyoyin tsaro sun ce Derya ya riƙa gudanar da tarurruka a ƙasashen Turai daban-daban da jami’an Mossad masu amfani da sunayen ɓoye kamar Luis, Jesus/Jose, Dr. Roberto/Ricardo, Dan/Dennis, Mark, Elly/Emmy da Michael.

Masu bincike na zargin cewa mutanen biyu sun riƙa tattara bayanai ta hanyar hulɗar zamantakewa da kasuwanci da Falasɗinawa masu sukar manufofin Isra’ila a yankin, sannan suna miƙa bayanai kan mutane, wurare da hanyoyin sadarwa ga leƙen asirin Isra’ila.

Ana kuma zargin Derya da ƙoƙarin samun izinin shiga Gaza, da yin binciken leƙen asiri kan wuraren ajiyar kaya a can, tare da aika hotuna ga Mossad.

 

 

 

Rumbun Labarai
Yadda Ma'aikatar Tsaro ta Turkiyya take taimakawa wajen rage tunzurin yanki ta bayan fage
An kawar 'yanta'adda 3 kusa ta ofishin jakadancin Isra'ila a Istanbul: Ministan Cikin Gidan Turkiyya
Turkiyya ta ƙaddamar da shirin jigilar kaya ta Saudiyya saboda rufe Mashigar Hormuz
Israila na ci gaba da kawo cikas ga duk wani ƙoƙarin kawo ƙarshen yaƙin Iran: Erdogan na Turkiya
'Masu gurɓataccen ra'ayi': Me ya sa ƙaruwar gudunmawar Turkiyya a NATO ke kaɗa hantar Isra'ila?
Ruwa na maye gurbin mai a matsayin arziki mafi muhimmanci: Erdogan na Turkiyya
Turkiya ta doke Kosovo inda ta samu damar shiga gasar cin kofin duniya ta 2026
Zero Waste: Ƙarƙashin jagorancin Emine Erdogan, duniya ta tuna da Ranar Kawar da Shara
Shugaban Hukumar Leƙen Asiri ta Turkiyya ya yi gargaɗi kan rikicin Iran na iya zama na duniya
Kare gaskiya na da matuƙar muhimmanci a 'zamanin labaran ƙarya': Daraktan Sadarwa na Turkiyya
An fara taron Stratcom 2026 a Istanbul yayin da hankalin duniya ke ƙara tashi da yaƙin watsa labarai
Baya ga warware rikice-rikice, Turkiyya na sauya yadda al’amura ke gudana a duniya
Fidan na Turkiyya ya yi jerin tattaunawa da takwarorinsa kan kokarin kawo karshen yakin Iran
Ƙasashen Gulf za su iya ‘ɗaukar mataki’ kuma yaƙin Iran yana iya watsuwa: Babban jami'in Turkiyya
China ta yaba wa Turkiyya, Saudiyya, Qatar kan rawa a tsagaita wuta tsakanin Pakistan da Afghanistan
Shugaba Erdogan ya girmama nasarar 'Canakkale' a yaƙin duniya na ɗaya
Tallafin NATO ga Turkiyya zai gwada ƙarfin ƙawancensu yayin tashin hankalin Gabas ta Tsakiya: masana
An daƙile makami mai linzami na Iran a kan hanyarsa ta kutsawa Turkiyya
Turkiyya ta tura jiragen yaƙi na F-16 shida Arewacin Cyprus yayin yaƙin Amurka da Isra'ila kan Iran
Turkiyya ta kira jakadan Iran, ta nuna damuwarta kan harba makami mai linzami a sararin samaniyarta