Teknofest: Ana yin zangon karshe na babban baje-kolin fasaha na Turkiyya

Baje-koli mai daukar hankali ne inda ake nuna jiragen sama  masu basira da gasar fasahohi da manhajoji da sauransu.

By Charles Mgbolu
Masu halartar taron sufurin jirage da sararin sama da fasaha wanda aka yi wa lakabi da TEKNOFEST a filin jirgin sama na Çiğli. Hoto: AA / Others

Daga Charles Mgbolu

An bude baje-kolin fasaha na Turkiyya da jiragen sama da aka yi wa lakabi da TEKNOFEST 2023 zango na uku kuma na karshe a ranar Laraba a birnin İzmir da ke kudu maso yammacin kasar.

Bikin kwana biyar din za a kammala shi a ranar 1 ga watan Oktoba, kuma tawagar fasaha ta Turkiyya (T3) ce ta shirya shi da hadin gwiwar Ma'aikatar Masana'antu da Fasaha ta Turkiyya.

Abu ne mai daukar hankali yadda aka baje-kolin jiragen sama da fasaha da manhajoji da yin taruka kan fannin ilimi da sauransu.

Bikin baje-kolin bana ya zo ne a muhimmin lokacin da Turkiyya take bikin cika shekara 100 da kafuwa.

Bikin na bana an yi shi ne daki-daki, inda aka fara yin zangon farko a birnin Istanbul a watan Afrilu, wanda mutum miliyan biyu suka halarta – abin da ba a taba ganin irinsa a baya ba.

An yi zango na biyu ne a birnin Ankara tsakanin ranar 30 ga watan Agusta zuwa ranar 3 ga watan Satumba, a filin jirgin saman Etimesgut, inda mutum 943,000 suka halarta.

Birnin İzmir yanzu yana cike da farin ciki yayin da yake fatan kafa tarihi lokacin baje-kolin a sararin samaniyarsa.

Za a yi bikin ne a filin jirgin saman Çiğli a İzmir kuma za a baje-kolin fasaha da jiragen sama da motoci da yin taruka kan fannin ilimi da sauran abubuwa masu kayatarwa.