| Hausa
WASANNI
1 minti karatu
Falconets ta Nijeriya ta lallasa New Caledonia da ci 10-1, ta kai zagayen gaba a gasar Kofin Duniya
Tawagar Nijeriyar ta mamaye wasan tun daga farko, inda ta ci 4-0 kafin a tafi hutun rabin lokaci, sun ƙara zura ƙwallaye shida bayan an dawo.
Falconets ta Nijeriya ta lallasa New Caledonia da ci 10-1, ta kai zagayen gaba a gasar Kofin Duniya
Tawagar Falconets ta Nijeriya ta lallasa New Caledonia da ci 10-1, ta kai zagayen gaba

Tawagar ƙwallon kafa ta mata ta Nijeriya, Falconets, ta kai zagayen ‘yan-16 a gasar cin Kofin Duniya ta FIFA 2026 ta mata ‘yan ƙasa da shekara 20.

Hakan ya biyo bayan lallasawar da ta yi New Caledonia da ci 10-1 a Poland ranar Lahadi.

Tawagar Nijeriyar ta mamaye wasan tun daga farko, inda ta ci 4-0 kafin a tafi hutun rabin lokaci.

Bayan dawowa daga hutu, Falconets ta ƙara zura ƙwallaye shida.

Ramotalahi Kareem da Winner David sun zura ƙwallaye uku kowacce. Yayin da Rebecca Adegbemile ta ci ƙwallaye biyu, sai kuma Seimeyeha Akekoromowei da Tosin Rafiu suka ci ƙwallo ɗaya kowacce.

New Caledonia ta ci ƙwallo ɗaya daf da ƙarshen wasan, amma hakan bai hana Nijeriya samun gagarumar nasara ba.

Wannan nasara ta kai Falconets matsayi na biyu a rukunin F, tare da tabbatar da gurbinta na zuwa zagayen ‘yan-16.

A baya, tawagar ta Nijeriya ta tashi da 0-0 da China, bayan da Sifaniya ta doke ta da ci 2-0 a wasan farko.

Tawagar Siyafiya ce ke jagorantar rukunin da maki tara, kuma tuni ta samu gurbin zuwa zagayen ‘yan-16.

Ana sa ran Falconets za ta kara da Ingila a zagayen gaba.

Rumbun Labarai
Ronaldo zai iya komawa tawagar Portugal idan yana so, in ji kocin ƙasar
Tirkashi: Real Madrid na so a ƙwace wa Barcelona kofuna 9, ta gabatar da ƙorafi mai shafi 50,000
Shugaban hukumar ƙwallo da kocin Portugal sun zauna don lallashin Ronaldo bayan ƙin saka shi a wasa
Barcelona ta fusata da Ancelotti kan raunin da Raphinha ya samu a wasan Brazil da Australia
An samu Manchester City da laifin keta dokokin kuɗi
Nijeriya da Ghana sun sha kashi a wasannin neman gurbin shiga Gasar AFCON ta 2027
Manyan kulob sun shirya wawason 'yanwasan Man City idan kotu ta kore ta daga Gasar Firimiya
Zidane ya yaba wa Turkiyya gabannin wasansa na farko a matsayin mai horar da tawagar Faransa
Taiwo ya maye gurbin Osimhen yayin da aka buɗe sansanin horaswa na Super Eagles
Kocin Super Eagles ya fitar da sunayen ‘yanwasan da za su buga wasanni a Satumba da Oktoba
Messi ya ci ƙwallonsa ta 100 a Inter Miami yayin da suka lashe Kofin Campeones
Mbappe ya ce ya ƙi sa rigar Ceuta yadda ya kamata ne don tausaya wa baƙin haure 'yan Morocco
Messi na shirin buga wa Argentina wasansa na ƙarshe
Masu ruwa da tsaki a ƙwallon ƙafar Nijeriya na taron tattauna hanyoyin kawo gyara
'A Maroko za a yi wasan ƙarshe na Kofin Duniya na 2030', in ji shugaban hukumar ƙwallon kasar
'An yi wa Arsenal fasha a wasansu da Aston Villa', in ji hukumar gasar Firimiya
NFF ta naɗa Eguavoen a matsayin kocin wucin-gadi na Super Falcons
An manta da Raphinha da Pedri cikin 'yanwasa 30 da za su iya lashe kyautar Ballon d'Or
Barcelona ta miƙa ƙoƙon-bara wajen masu zuba jari don neman kuɗin gyaran filin wasa
Turkiyya ta kuma lashe kofin gasar volleyball ta mata ta nahiyar Turai