| hausa
TURKIYYA
3 MINTI KARATU
An raunata 'yan sanda biyu a harin ta'addanci da aka kai birnin Ankara na Turkiyya
'Yan sanda biyu suka dan ji rauni a harin, wanda ya faru da misalin 9:30 na safe, wato 0630 agogon GMT, in ji Ministan Cikin Gida na Turkiyya Ali Yerlikaya.
An raunata 'yan sanda biyu a harin ta'addanci da aka kai birnin Ankara na Turkiyya
Titin Ataturk an rufe shi sakamakon cunkoson ababen hawa biyo bayan tashin bam din wanda ke kusa da daya daga cikin kofofin shigar Babbar Majalisar Kasar. Hoto/ AA
1 Oktoba 2023

Akalla ‘yan sanda biyu aka raunata a lokacin da wasu ‘yan ta’adda suka tayar da bam a gaban Babban Ofishin Tsaron Turkiyya da ke Ma'aikatar Cikin Gida a Ankara, inda daya daga cikin ‘yan ta’addan ya kashe kansa da bam din.

“’Yan ta’adda biyu, wadanda suka zo a wata karamar motar haya a gaban kofar shiga Babban Ofishin Tsaro, sun kaddamar da harin ta’addanci.

Daya daga cikinsu ya kashe kansa,” kamar yadda Ali Yerlikaya ya bayyana a ranar Lahadi. Yerlikaya ya bayyana cewa an ji wa ‘yan sanda biyu ciwo a yayin harin duk da cewa ciwon ba mai tsanani bane.

Harin ya faru da misalin karfe 9:30 na safe, wato 0630 agogon GMT. An ji karar harin a gaban Ma’aikatar Cikin Gida ta Turkiyya wadda ke a tsakiyar Ankara.

Bayan karar bam din da harbe-harben bindiga da aka ji kusa da ginin ma’aikatar da ke Kizlay, wanda shi ne babban wuri a birnin da ke gundumar Cankay, ‘yan sanda sun kara tsaurara tsaro a wurin.

Titin Ataturk an rufe shi sakamakon cunkoson ababen hawa biyo bayan tashin bam din wanda ke kusa da daya daga cikin kofofin shigar Babbar Majalisar Kasar.

An tura ‘yan sanda na musamman zuwa wurin da lamarin ya faru. Haka jami’an kashe gobara da kuma likitoci sun isa wurin.

Za a bude Babbar Majalisar kasar da rana bayan shafe hutun watanni uku.

Ofishin Babban Mai Shigar da Kara na Ankara ya kaddamar da bincike kan harin na ta’addanci.

MAJIYA:TRT World
Rumbun Labarai
Sojojin Turkiyya 20 sun yi shahada a hatsarin jirgin soji na dakon kaya a Georgia: Ma’aikatar Tsaro
Jirgin dakon kaya na sojin Turkiyya ya yi hatsari a iyakar Georgia-Azerbaijan dauke da jami'ai 20
Turkiyya na jimamin tunawa da rasuwar Ataturk shekara 87 da suka wuce
Nasarar da aka samu a yankin Karabakh na Azerbaijan babbar nasara ce ga yankin Caucasus: Erdogan
Turkiyya ta yi umarnin kama Firaministan Isra'ila Netanyahu da wasu mutane kan kisan kiyashi a Gaza
Turkish Airlines ya sayi hannun jari na dala miliyan 355 a kamfanin Air Europa na Spain
Erdogan ya yi Allah wadai da kashe fararen-hula a birnin Al Fasher na Sudan
Za a gudanar da tattaunawa a Istanbul kan yarjejeniyar tsagaita wutar Gaza da matsalolin jinƙai
Tsarin duniya na yanzu ya fi ba da fifiko kan iko fiye da adalci: Babban Daraktan TRT Sobaci
Hamas ba ta da nukiliya, amma Isra'ila na da su: Erdogan ya nemi Berlin ta ɗauki mataki kan Tel Aviv
Ana shirin fara taron TRT World Forum karo na 9 a Istanbul
Cikin hotuna: Yadda aka yi bukukuwa a duk faɗin kasa na cikar Ranar Jamhuriya ta Turkiyya ta 102
Turkiyya ta yi kira a tsagaita wuta nan-take a yaƙin da ake yi a birnin Al Fasher, Sudan
Turkiyya za ta mika wa dakarunta tankar yaki ta Altay da aka samar da yawa a karon farko
Kungiyar ta'addanci ta PKK ta sanar da janyewa baki ɗaya daga Turkiyya
Babu wani lissafin siyasa ko na tsaro da zai yiwu a duniya ba tare da Turkiyya ba: Erdogan
Rumfar Karfe: Fasahar Turkiyya ta cikin gida mai aiki da Ƙirƙirarriyar Basira a sabon zamanin tsaro
Shugaba Erdogan ya shirya ziyartar yankin Gulf don haɓaka alaƙar tattalin arziki da ƙawance
Turkiyya ta yi maraba da yarjejeniyar tsagaita wutar Afghanistan da Pakistan
An Fara Taron Yaki da Shara na ‘Zero Waste’ a Istanbul karkashin jagorancin Emine Erdogan