Rundunar sojin Nijeriya za ta yi bincike a kan zargin rashin ciyar da dakarunta da ke filin daga
Rundunar ta ce yana da muhimmanci sosai al’umma ta san cewa ta damu da duk abin da ya shafi kula da walwalar dakarunta.
Rundunar sojin Nijeriya ta ce za ta gudanar da cikakken bincike a kan zargin da aka jawo hankalinta a kansa, na cewa ba a ciyar da dakarunta da ke filin daga isasshen abinci.
A wata sanarwa da rundunar ta fitar ranar Talata da maraice mai dauke da sa hannun daraktan yada labaranta Birgediya Janar Onyema Nwachukwu, ta ce yana da muhimmanci sosai al’umma ta san cewa rundunar ta damu da duk abin da ya shafi kula da walwalar dakarunta.
“Rundunar sojin Nijeriya ta dauki wadannan zarge-zarge da muhimmanci sosai kuma babban hafsan rundunar sojin kasa Laftanal Janar Taoreed Lagbaja ya ba da umarnin yin duba don gano girman lamarin da kuma abubuwan da suka jawo shi,” in ji sanarwar.
Zargin yana magana ne a kan rashin ciyar da dakarun wadanda ke yaki da kungiyar Boko Haram a yankin arewa maso gabashin kasar isasshen abinci mai gina jiki.
Sanarwar ta ce “a ko yaushe rundunar soji na fifita walwalar dakarunta da ya hada da abincinsu. Akwai cikakken tsari na tabbatar da cewa dakaru na samun isasshe kuma lafiyayyen abinci, musamman ma ga wadanda suke fagen daga, kuma ana shirya abincin cikin tsananin kula da kuma inganci.”
Duk da cewa rundunar sojin ta amince cewa mai yiwuwa akwai wadansu ‘yan matsaloli da ake iya samu, “to ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen magance su.”
“Tuni aka kaddamar da binciken cikin gida don gano gaskiyar da ke cikin zarge-zargen. Za mu yi duba na tsanaki a kan tsarin samar da abincin, da ingancin abincin da ake ba su da ma duk wani abu da ka iya lalata tsarin.
Ladabtarwa
Rundunar sojin ta kuma sha alwashin daukar matakan ladabtarwa kan duk wani da aka same shi da hannu a yin wasarere ko bata tsarin bai wa dakaru abinci.
Sannan ta nemi dakarun nata da su dinga gabatar da kowane irin korafi ko damuwa da suke da su a kan abin da ya shafi ciyarwa.
A karshe rundunar sojin ta tabbatar da ci gaba da bibiyar lamarin da kuma ganin dakarunta, musamman wadanda ke fagen daga na samun dukkan abubuwa da kulawar da suke bukata don su yi aikinsu yadda ya dace.
“Za mu tabbatar da cewa ana ciyar da dakarunmu yadda ya dace ta yadda za su samu karfin kula da kasarmu,” in ji sanarwar.