An sace wasu daliban Jami'ar Dutsin-Ma a Jihar Katsina
Jami'in hulda da jama'a na jami'ar ya ce lamarin ya faru ne a ranar Laraba da safe a gidajen da dalibai ke zama a wajen makarantar.
'Yan bindiga sun sace wasu daliban Jami'ar Tarayya ta Dutsin-Ma da ke Jihar Katsina a arewacin Nijeriya, kamar yadda ma magana da yawun jami'ar Malam Habibu Umar ya tabbatar wa TRT Afrika.
Jami'in ya ce lamarin ya faru ne a ranar Laraba da safe a gidajen da dalibai ke zama a wajen makarantar.
"Ba dakunan kwanan dalibai da ke cikin makaranta maharan suka shiga ba, a rukunin gidaje masu zaman kansu da dalibai ke kama haya ne 'yan bindigar suka je suka sace daliban," in ji Malam Habibu.
Amma ya ce a yanzu hukumar makaranta ba za ta iya tabbatar da yawan daliban da aka sace ko jinsinsu ba har sai ta kammala binciken da take yi.
Wasu labaran masu alaka
- 'Yan bindiga sun sace daliban Jami'ar Tarayya ta Gusau
- Batun sace daliban Gusau ya tayar da kura a arewa
Wannan ne karo na biyu da aka sace dalibai a makaranta a cikin kasa da mako biyu a Nijeriya, inda kwanan nan aka sace wasu daliban mata a Jami'ar Tarayya da ke Gusau a Jihar Zamfara.
Sannan a ranar Litinin ma 'yan bindiga sun shiga Jami'ar Usman Danfodio ta Sokoto amma Allah Ya takaita ba su sace kowa ba sai kayan abinci.