| hausa
DUNIYA
3 MINTI KARATU
Kudin-cizo ya tilasta wa Faransa rufe makarantu
Ministan Ilimin Faransa Gabriel Attal ya ce suna fargaba matsalar kudin-cizo za ta bazu zuwa wasu yankunan.
Kudin-cizo ya tilasta wa Faransa rufe makarantu
Gwamnatin Faransa ta gudanar da taruka daban-daban a wannan makon domin gano girman matsalar yaduwar kudin-cizo a yayin take karbar bakuncin Gasar Kwallon Rugby ta Duniya / Hoto: Reuters
7 Oktoba 2023

Kudin-cizo ya tilasta wa Faransa rufe makarantu bakwai sakamakon fargabar bazuwarsa a yankuna daban-daban, kamar yadda Ministan Ilimi na kasar Gabriel Attal ya bayyana ranar Juma'a.

"An gano kudin-cizo a makarantu da dama... Ina ganin sun kai makarantu 17, kuma a yanzu da nake magana da ku, an rufe makarantu bakwai saboda wannan matsala," a cewar Attal a hira da gidan talbijin nan France 5.

Gwamnatin Faransa ta gudanar da taruka daban-daban a wannan makon domin gano girman matsalar yaduwar kudin-cizo a yayin take karbar bakuncin Gasar Kwallon Rugby ta Duniya sannan take shirin karbar bakuncin Gasar Olympics ta 2024.

Tun da farko, Ministan Ilimi ya aike wa da kamfanin dillancin labarai na AFP yana cewa an rufe makarantu biyar masu dalibai 1,500.

A farkon makon nan, hukumomi sun sanar da rufe makarantu biyu -- daya a Marseille da daya a garin Villefranche-sur-Saone da ke wajen birnin Lyon na kudu maso gabashin Faransa -- domin raba su da kudin-cizo.

"Muna da makarantu kusan 60,000 kuma wannan lamari ya shafi gomman makarantu ne kawai, amma gaskiya lamarin yana karuwa," a cewar Attal. "Ana bukatar daukar matakan gaggawa, don haka za mu yi feshin magani bab dare babu rana."

Ya kara da cewa sun hada gwiwa da Ma'aikatar Lafiya da hukumomin kul da kiwon lafiya na larduna kuma an "amince da wasu kamfanoni" da "shugabannin makarantu za su rika tuntuba domin daukar mataki nan-take."

Labari mai alaka: Algeria za ta sa ido don hana kudin-cizo shiga kasarta 'daga Faransa'

Ana sa rai za a sake bude wani dakin karatu wato laburare da ke Amiens ranar Asabar bayan an rufe shi tsawon kwanaki saboda an gano kudin-cizo a wuraren da mutane suke karatu, a cewar shugabar birnin Brigitte Foure a hira da AFP.

Ta kara da cewa karnukan da ke sansano abubuwa ba su ji duriyar kudin-cizo ba a dakin karatun bayan an yi masa feshin magani.

An yi amannar cewa ana samun kudin-cizo a akalla gida daya cikin goma a fadin Faransa a shekarun baya-bayan nan, kuma galibi yana bukatar feshin magani sau da dama wanda da ke bukatar kashe kudin da yawa kafin ya mutu.

Aan gano kudin-cizo a tashar jiragen kasa ta Paris da tashar jiragen kasa masu gudun-tsiya da kuma filin jirgin sama Charles De Gaulle.

MAJIYA:AFP
Rumbun Labarai
Zinarin da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ke shigarwa ƙasarta daga Sudan ya ƙaru yayin da ake yaƙi
COP30: Manyan masu gurbata muhalli na duniya ba su je taron sauyin yanayi na Brazil ba
Rasha ta ce tana sa ido kan Nijeriya bayan barazanar da Trump ya yi ta kai hari kasar
Zohran Mamdani: Matashi Musulmi na farko ya lashe zaɓen Magajin Birnin New York
Yadda amfani da magungunan antibiotic barkatai ya sa cututtuka suka zama makamai
Rundunar Sojin Ruwan Pakistan ta kama mugwayen ƙwayoyi na dala biliyan ɗaya a Tekun Arebiya
An gano sauro a karon farko a ƙasar Iceland
Yadda hukumomi a India suke farautar Musulmai da suke cewa 'Ina son Annabi Muhammad'
Putin ya gargaɗi Trump cewa bai wa Ukraine makamai mai linzamin Tomahawk zai jawo matsala tsakaninsu
Abin da muka sani game da mummunar arangamar kan iyaka tsakanin sojin Pakistan da Afganistan
Waiwayen 1903: An taɓa yi wa Yahudawa tayin Afirka, kamar yadda ake so a mayar da Falasɗinawa yanzu
An naɗa Sarah Mullally mace ta farko Shugabar Cocin Ingila
Yadda mutuwar ɓauna a turmutsutsu ke sauya salon farautar manyan namun dawa
An tsinci gawar jakadan Afirka ta Kudu a Faransa a wajen otal a birnin Paris
Babban Alkalin Kotun Amurka ya dakatar da umarnin Trump na korar ma’aikatan VOA
UNGA: Yadda ta kaya a taron 'nuna wa juna yatsa da huce haushi' na Majalisar Dinkin Duniya
Yadda jami'an diflomasiyyar duniya suka fice daga Zauren UNGA yayin da Netanyahu zai yi jawabi
Jawabin Trump a taron MDD ya fito da sakamakon nuna ƙyamar Musulunci a duniya
An yanke wa tsohon Shugaban Faransa Sarkozy hukuncin shekara biyar a gidan yari
UNGA 80: Trump ya yi alkawarin hana Isra'ila shirin ƙwace Yammacin Kogin Jordan