| Hausa
AFIRKA
3 MINTI KARATU
Ba mu janye daukaka karar da muka yi a zaben gwamnan Kano ba – INEC
INEC ta ce ba ta umarci jami'inta na Kano ya rubuta wasikar janye karar da ta daukaka ba, tana mai cewa za ta ci gaba da shari'ar kuma tuni ta gargade shi.
Ba mu janye daukaka karar da muka yi a zaben gwamnan Kano ba – INEC
Hukumar zaben ta bukaci jama’a su yi watsi da rahotannin cewa ta janye daga daukaka karar.,/Hoto:Reuters / Others

Hedikwatar Hukumar zabe mai zaman kanta a Nijeriya ta ce ba da yawunta wani jami’inta na Kano ya janye karar da ta daukaka game da zaben gwamnan jihar ba.

Wata sanarwa da Kwamishinan hukumar na kasa kuma shugaban sashen wayar da kan jama’a da masu zabe Sam Olumekun ya fitar ranar Asabar ta ce hukumar tana nan daram a kan karar da ta daukaka bayan kotun sauraren kararrakin zabe ta ayyana Nasiru Yusuf Gawuna na jam’iyyar APC a matsayin gwamnan Kano.

INEC ta kara da cewa an jawo hankalinta game da wasu rahotanni da ke cewa jami’inta da ke kula da harkokin shari’a na Kano ya rubuta wasikar janye karar da ta daukaka bayan kotu ta soke zaben Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP, tana mai cewa ba ta umarce shi ya dauki matakin ba.

“Muna so mu bayyana karara cewa ba mu umarci a rubuta wasikar ba. An janye ta kuma an gargadi wannan jami’i,” in ji INEC.

Hukumar zaben ta bukaci jama’a su yi watsi da rahotannin da ke cewa ta janye daga daukaka karar.

“Muna so mu fada a fili cewa duk karar da aka sanya INEC a cikinta, ya zama wajibi hukumar ta saurare ta. Don haka mun umarci lauyoyinmu su ci gaba da (wannan shari’a) kamar yadda dokar hukumar ta tanada,” a cewar INEC.

Tun da farko wasu rahotanni da aka rika watsawa a soshiyal midiya sun ce INEC ta janye daga daukaka karar, lamarin da ya jawo zazzafar muhawara tsakanin ‘yan APC da NNPP da ma wasu jama’a na jihar ta Kano.

MAJIYA:TRT Afrika
Rumbun Labarai
Ghana ta kama mutum 19 kan zargin laifukan intanet tare da gano damfarar dala miliyan 8.3
Nijar ta ayyana mummunan haɗarin muhalli bayan malalar mai
Gwamnatin Nijar ta kafa kwamitin magance ƙaranci da basussuka a ɓangaren man fetur
Aljeriya ta kama ‘yan Maroko 61 bisa zargin kitsa mata zagon-ƙasa
An miƙa wa 'yan kwangila ayyukan fara gina azuzuwa 357 a jihar Dosso ta Nijar
Gwamnatin Nijar ta yi watsi da buƙatar ƙarin farashin man fetur a ƙasar
MƊD: An raba mutane miliyan huɗu da gidajensu a Burkina Faso da Mali da Nijar
Sojoji na cikin mutum 71 da aka kashe a Sudan ta Kudu bayan mummunar arangama
Faransa ta kori jami’an leƙen asirin Nijar biyu daga ƙasarta
'Yar Afirka ta Kudu Navi Pillay ta ci kyautar Nobel ta Zaman Lafiya ta shekarar 2026
Rikicin wakilci a yanki: Me ke ta'azzara rikicin Ethiopia-Eritrea?
Haɗuran mota sun yi sanadin mutuwar mutum 2,151 a Ghana cikin watanni tara - Rahoton MTTD
Ethiopia ta nemi a janye dakarun Eritrea 'nan-take' daga ƙasarta
Ghana da FBI sun kama mutum 130 da ke da alaƙa da zambar $10m
Babban kwamanda a mayaƙan RSF ya koma rundunar sojin Sudan tare da mayaƙa 300
Burkina Faso za ta sauya darussan makarantu don 'kawar da tsarin mulkin mallaka' a fannin ilimi
Ghana za ta nemi shiga ƙungiyar BRICS
Gambia ta sayi manyan injinan samar da wutar lantarki  biyu domin magance matsalar wuta a ƙasar
Shugaban Masar ya soki tsoma bakin ƙasashen waje a harkokin Afirka
Ƙungiyar Tarayyar Afirka ta musanta ɗora wa Masar laifin rikin Ethiopia bayan ƙin yardar Alƙahira