Kai hari asibiti mafi kololuwar cin zali da take darajar dan'adam ne: Shugaba Erdogan
Ma’aikatar Lafiya ta Falasɗinu ta ce aƙalla mutum 500 harin saman da Isra’ila ta kai ya shafa a Asibitin Al Ahli Baptist da ke Gaza.
Shugaban ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya yi kira ga dukkan mutanen duniya da su ɗauki matakin dakatar da “munanan hare-haren da ba a taɓa ganin irinsu ba” da Isra’ila ke kai wa Gaza.
“Kai hari kan asibitin da mata da yara da sauran fararen hular da ba su ji ba ba su gani ba ke ciki shi ne mafi kololuwar cin zali da take darajar dan'adam na hare-haren Isra'ila,” in ji Erdogan a shafinsa na X a ranar Talata, jim kadan bayan kai harin sama da Isra’ila ta yi a Asibitin Al Ahli da ke birnin Gaza da aka yi wa ƙawanya, inda fiye da Falasɗinawa 500 suka mutu.
Ma’aikatar Lafiya ta Falasɗinu ta ce aƙalla mutum 500 harin saman da Isra’ila ta kai ya shafa a Asibitin Al Ahli Baptist da ke Gaza.
“Har yanzu akwai ɗaruruwan mutane a ƙarƙashin ɓaraguzai,” ta ƙara da cewa.
Ofishin watsa labarai na gwamnatin Hamas da ke Gaza ya bayyana harin a matsayin “laifin yaƙi”.
“Akwai ɗaruruwan marasa lafiya da waɗanda suka ji rauni a kwance a cikin asibitin a lokacin, da kuma mai yiwuwa wasu da ke samun mafaka a wajen waɗanda suka rasa muhallansu sakamakon sauran hare-haren da ake kai wa,” in ji sanarwar.
‘Kai hari asibiti mummunan laifi ne’
“Kai hari a kan asibiti mummunan laifi ne. Yi wa mutanen da ke kwance suna jinya kisan kiyashi ya shallake tunani. Kai hari kan fararen hula amfani ne da dabarun ta’addanci, gaskiyar magana kenan,” kamar yadda Daraktan Sadarwa na Turkiyya Fahrettin Altun ya wallafa a shafinsa na X.
“Ba za a lamunci hare-haren rashin tausayi kamar irin wanda aka kai Asibitin Baptist a Birnin Gaza ba. Dubban fararen hular da ba su ji ba, ba su gani ba sun azabtu sosai. Dole ne a dakatar da hakan. Faƙat,” ya ƙara da cewa.
“Kamar yadda Shugaba Erdogan ya bayyana, dole ne duniya baki ɗaya ta taru don hana Isra’ila aikata munanan ayyuka a kan fararen hula. Ana kai wa fararen hula da mata hari, wannan mummunan lamari ne da babu tausayi da jinƙan ɗan’adam da ke da daraja a wajenmu.”
“Dole ne Isra’ila ta dakatar da kisan kiyashin da take yi a kan fararen hula. Dole ne a daina musgunawa Falasdinwa ta hanyar tsorata su da hana su abinci da kai musu hare-hare.
"Dole a daina cutar da marasa lafiya da tsofaffi. Dole a daina kai wa Gaza hare-hare. Dole ne duniya ta tashi tsaye ta hana wannan zubar da jinin,” ya ƙara da cewa.
Turkiyya ta yi Allah wadai da kakkauwar murya da “harin zalincin”
Turkiyya ta yi Allah wadai da kakkausar murya kan“mummunan harin” da aka kai Asibitin Al Ahli Baptist a Gaza, wanda ya kashe ɗaruruwan Falasɗinawa tare da jikkata wasu ɗaruruwan, kamar yadda Ma’aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta fada a wata sanarwa.
“Muna miƙa saƙon ta’aziyyarmu ga ƴan uwanmu Falasɗinawa da suka rasa iyalansu a wannan hari tare da yi wa waɗanda suka jikkata fatan samun sauƙi,” a cewar sanarwar.
“Ya zama wajibi a gurfanar da duk wanda ke da hannu a kai wa fararen hula da asibitoci da makarantu hare-hare a gaban kotun ƙasa da ƙasa kan nuna rashin tausayi da jinƙai,” ta ƙara da cewa.