Kenya ta kama ɗan China kan yunƙurin safarar tururuwa fiye da 2,000 da ya ɓoye a cikin kwalabe
Masu bincike sun ce sun gano tururuwa 2,238, ciki har da 1,948 da aka nade a cikin kwalaben gwaji, yayin da sauran ke cikin sunƙin takardar tissue uku.
An kama wani mutum da fiye da tururuwa 2,200 masu rai a cikin jakarsa a babban filin jirgin sama na Nairobi a wannan makon, a daidai lokacin da ake samun ƙaruwar safarar irin waɗannan ƙwari a Kenya.
Dan ƙasar China Zhang Kequn, mai shekaru 27, an kama shi a Filin Jirgin Sama na Jomo Kenyatta a ranar Talata yayin da yake ƙoƙarin barin ƙasar, a cewar takardun kotu da aka gabatar a ranar Alhamis.
Jami’an shige da fice sun nuna cewa an sanya wa fasfo ɗin Zhang "stop order", wato umarnin hana shi tafiya, bayan ya tsere a yayin yunƙurin kama shi a Kenya a bara.
Masu sha’awar tururuwa na biyan kuɗaɗe masu yawa don samunsu inda suke saka su a cikin ƙananan fararen kwalabe, inda ta haka suke sa ido kan ɗabi’u da yadda ƙwarin ke gudanar da rayuwarsu.
A bara, an yi wa maza huɗu hukuncin tara ta dala 7,700 kowannesu saboda ƙoƙarin safarar dubban tururuwa masu muhimmanci ga tsarin muhalli na Kenya, a shari’ar da masana suka ce ta nuna sauyi daga sata ta halittu kamar ƙashin giwa zuwa nau’ukan da ba a sani ba sosai.
Masu bincike sun ce binciken jakar Zhang ya sa an dawo da tururuwa 2,238, ciki har da 1,948 da aka nade a cikin kwalaben gwaji, yayin da sauran ke cikin sunƙin takardar tissue uku.
Sun ce Zhang ya kasance a Kenya na makonni biyu kuma ya ambaci abokan haɗin gwiwa guda uku da suka samar masa da tururuwar.
Hukumar Kula da Dabbobin Daji ta Kenya ta shaida wa kotu cewa tana bukatar ƙarin lokaci don kammala bincike, ciki har da yin bincike kan wayar iPhone da kwamfuta ta MacBook da aka kwato daga Zhang.
Hukumar ta ce an kama irin wannan tururuwar a Bangkok a ranar Talata wandda ta fito daga Kenya, abin da ke nuna yiwuwar kasancewar wata babbar hanyar safarar tururuwa da aka tsara.