'Ba da yawunmu ake yin kisan kiyashi a Gaza ba': Yahudawan New York
'Yan sanda sun kama daruruwan mutane bayan wata kungiyar Yahudawa mai suna Jewish Voice for Peace, wacce ke kyamar tsattsauran ra'ayin Yahudanci, ta gudanar da zanga-zanga "mafi girma a New York City da aka yi a shekaru 20"
'Yan sanda sun kama daruruwan Yahudawa a birnin New York na Amurka bayan wata kungiyarsu ta gudanar da zanga-zanga a babban zauren tashar jiragen kasa ta Grand Central don kyamar hare-haren da Isra'ila ke kai wa a Gaza.
Ofishin 'yan sandan New York ya ce an kama akalla mutum 200 ranar Juma'a, ko da yake masu zanga-zangar sun ce wadanda aka kama sun zarta 300.
Hotunan da aka fitar na zanga-zangar sun nuna jerin gwanon matasa sanye da bakaken riguna da aka rubuta "Ba da yawunmu ake kisa ba" da kuma "A tsagaita wuta nan-take" wadanda 'yan sanda suka daura musu ankwa.
Kungiyar Yahudawa ta Jewish Voice for Peace-New York City ce ta dauki nauyin zanga-zangar wadda ta ce dubban mambobinta sun halarta, inda suka rufe babbar hanyar shiga tashar jirgin kasan.
Hotuna sun nuna yadda masu zanga-zangar suka cika makil a cikin tashar jirgin kasan inda wasu kwalayen da suka rike aka rubutua "Ya kamata a bai wa Falasdinawa 'yanci."
'Rayuwar Falasdinawa da Isra'ilawa daya ce'
Limaman Yahudawa sun bude taron zanga-zangar ne da kunna kyandira na ranar Shabbat da kuma yin addu'o'i da aka fi sani da kaddish kan wadanda suka mutu.
"Duk da yake Shabbat rana ce ta hutu, mu ba za mu huta ba ganin yadda ake yin kisan kiyashi da yawunmu," in ji Limami May Ye, a sanarwar da wadanda suka gudanar da zanga-zangar suka fitar.
"Rayuwar Falasdinawa da Isra'ilawa daya ce, kuma za a samu tsaro ne kawai idan aka yi adalci da daidaito da kuma bayar da 'yanci ga kowa."