Za mu nuna wa duniya cewa Isra'ila ta aikata laifukan yaki: Erdogan

"Isra'ila na bin Kasashen Yamma bashi amma ba ta bin Turkiyyya. Shi ya sa muke magana ba tare da tsoro ba," in ji Shugaba Erdogan a lokacin da yake jawabi ga gangamin goyon bayan Falasdinawa da ke Gaza.

By Mustapha Kaita
Dubban mutane ne suka taru a filin jirgin Ataturk na Istanbul domin nuna goyon baya ga Falasdinawa: AA / AA

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya bayyana cewa kasarsa ta soma shirin nuna wa duniya cewa Isra'ila ta aikata laifukan yaki, a daidai lokacin da dubban mutane suke gangami da kuma nuna goyon baya ga Falasdinu.

"A daidai lokacin da muke daga muryoyinmu ga duniya muke shaida musu jin dadinmu kan cikarmu shekara 100 da zama Jahmuriya a gobe, a yau muna magana kan abin da ke mana ciwo a zukatanmu kan Gaza," in ji Shugaba Erdogan a lokacin da yake jawabi ga gangamin da ake yi a filin jirgin Ataturk a ranar Asabar.

Hotuna da bidiyo daga filin jirgin sun nuna mutane daga wurare da dama suna dauke da tutocin Turkiyya da na Falasdinu, wasu na saka maka-wuya inda aka rubuta, "Dukanmu Falasdinawa ne," "A kawo karshen kisan kiyashi, a bar yara su rayu" "Sannan a zama murya ga yaran Falasdinawa."

"Ya Gaza da ke Falasdinu take a 1947? Ya take a yau? Isra'ila ta ya kuka je can? Ta ya kuka shiga? Ku 'yan mamaya ne, ku kungiya ce," in ji Erdogan, inda ya bayyana cewa Turkiyya za ta gabatar da Tel Aviv ga duniya a matsayin wadda ta aikata laifukan yaki.

Ana gudanar da kisan kiyashi mummuna a Gaza, kamar yadda ya bayyana, inda yake kara tambaya kan yara da tsofaffi nawa da ba su ji ba su gani ba za a kara kashewa kafin a tsagaita wuta.

A yayin da yake caccakar Kasashen Yamma kan irin goyon bayan da suka nuna wa Isra'ila da kuma yadda suka yi amfani da kafafen watsa labarai domin halatta kisan kiyashin mutanen da ba su da laifi a Gaza, Erdogan ya jaddada cewa goyon bayan Turkiyya ga Falasdinu inda ya ce: "Isra'ila na bin Kasashen Yamma bashi amma ba ta bin Turkiyyya. Shi ya sa muke magana ba tare da tsoro ba."

"Littafin zunubai na Kasashen Yamma ya sake wuce gona da iri," kamar yadda ya kara da cewa, inda ya ce Isra'ila ba za ta iya aikata irin wannan zaluncin ba tare da taimakon Kasashen Yamma ba.

'Ba yaki tsakanin tsara ba ne'

Shahararren mawakin nan na duniya Yusuf Islam wanda aka fi sani da Cat Stevens shi ma ya yi jawabi a lokacin gangamin goyon bayan Falasdinawa kan "tayar da bam kan iyalai da ba su ji ba su gani ba, da gidajensu musamman kananan yara wadanda su ne rabin wadanda aka kashe".

Labari mai alaka: Isra’ila na kai hare-hare Gaza ne da 'nufin aikata laifukan yaki' — Fahrettin Altun

Ya gode wa Turkiyya kan "tsayawa yadda ya kamata" dangane da halin da ake ciki a Gaza.

"Wannan ba yaki bane tsakanin wadanda karfi ya zo daya. Idan muka kalli irin harin da aka kai a ranar 7 ga watan Oktoba da kuma yadda sojoji suka mayar da martani, ya wuce a yi kwatance," in ji Islam.

Ya bukaci yan Isra'ila da su tuna abin da aka ce a cikin Attaurah: Ku tuna asalin sakon da ubangiji ya aiko muku: Kada ku yi kisa, kada ku yi sata, kada ku nemi kayayyakin makwaftanku.' Wadannan su ne dokokin da Annabi Musa ya koya wa duniya. Me ya sa ba ku bin su?"

Tsawon makonni uku, Isra'ila ta kaddamar da hare-hare ba kakkautawa ta sama da kasa kan Gaza, inda ta yi wa birnin baki daya kawanya da kuma toshe duk wasu hanyoyi da za a shigo da abinci da fetur da magunguna.

Akalla Falasdinawa 7,326 aka kashe a yayin hare-haren, inda kaso 70 cikin 100 mata ne da yara, kamar yadda alkaluman hukumomi suka tabbatar.

A ranar Juma'a, Isra'ila ta katse hanyoyin sadarwa da na intanet a Gaza da ta mamaye, inda ta hana jama'ar birnin wadanda ba su da yawa saduwa da sauran jama'ar duniya.