| Hausa
WASANNI
3 MINTI KARATU
An sace iyayen dan wasan Livepool Luis Diaz
Kafafen watsa labarai na kasar sun ce Luis Manuel Diaz da Cilenis Marulanda sun je gidan mai ne yayin da masu garkuwa da mutane suka sace su.
An sace iyayen dan wasan Livepool Luis Diaz
Diaz, wanda ya buga wa Colombia sau 43, ya tafi Liverpool daga Porto a shekarar da ta wuce. / Hoto: AP / Others

An ceto mahaifiyar dan wasan Liverpool Luis Diaz daga hannun masu garkuwa da mutane ranar Asabar amma har yanzu ana neman mahaifinsa, a cewar shugaban kasar Colombia Gustavo Petro.

Petro ya wallafa sako a shafinsa na X, wanda a baya ake kira Twitter, cewa an ceto mahaifiyar Diaz a yankin Barrancas da ke arewacin Colombia.

"Muna ci gaba da neman mahaifinsa," in ji shugaban kasar.

Ofishin antoni janar na Colombia ya ce yana aiki tukuru kan batun.

"Daga lokacin da ofishin antoni janar ya samu labarin sace mahaifan dan wasan Colombia Luis Diaz a Barrancas ko La Guajira, tawagar kwararru ta masu shigar da kara da 'yan sanda da sojoji ta dukufa aiki domin gano inda wadannan mutane suke, da kuma gano wadanda suka sace su," a cewar sakon da ofishin ya wallafa a shafin X.

Kafafen watsa labarai na kasar sun ce Luis Manuel Diaz da Cilenis Marulanda sun je gidan mai ne yayin da masu garkuwa da mutane suka sace su.

Shugaban 'yan sandan kasar Janar William Salamanca, ya ce ya tura jami'an leken asiri da wasu jami'an tsaro domin kubutar da mutanen biyu.

Gwamnan La Guajira, Diala Wilches, ta yi tir da sace mahaifan dan wasan.

"Muna kira ga masu garkuwa da mutanen su sake su nan-take cikin koshin lafiya," in ji ta.

Dan wasan na Liverpool da Colombia, mai shekara 27, bai ce komai game da batun ba amma kungiyarsa ta fitar da sanarwa ranar Lahadi tana mai cewa tana "sane da abin da ke faruwa game da mahaifan Luis Diaz a Colombia".

"Muna fata za a warware matsalar cikin lumana kuma da wurwuri," kamar yadda kungiyar ta bayyana. "Kafin nan, kwanciyar hankalin dan wasan ita ce babbar damuwarmu."

Diaz, wanda ya buga wa Colombia sau 43, ya tafi Liverpool daga Porto a shekarar da ta wuce.

MAJIYA:AFP
Rumbun Labarai
Messi na shirin buga wa Argentina wasansa na ƙarshe
Masu ruwa da tsaki a ƙwallon ƙafar Nijeriya na taron tattauna hanyoyin kawo gyara
Falconets ta Nijeriya ta lallasa New Caledonia da ci 10-1, ta kai zagayen gaba a gasar Kofin Duniya
'A Maroko za a yi wasan ƙarshe na Kofin Duniya na 2030', in ji shugaban hukumar ƙwallon kasar
'An yi wa Arsenal fasha a wasansu da Aston Villa', in ji hukumar gasar Firimiya
NFF ta naɗa Eguavoen a matsayin kocin wucin-gadi na Super Falcons
An manta da Raphinha da Pedri cikin 'yanwasa 30 da za su iya lashe kyautar Ballon d'Or
Barcelona ta miƙa ƙoƙon-bara wajen masu zuba jari don neman kuɗin gyaran filin wasa
Turkiyya ta kuma lashe kofin gasar volleyball ta mata ta nahiyar Turai
An yanke wa Tiger Woods hukuncin haramcin tukin mota tsawon shekaru 5 saboda tuki cikin maye
Muhimman batutuwa game da ritayar Messi daga tawagar Argentina
Sakon Lionel Messi na yin ritaya daga buga kwallo a matakin kasa-da-kasa
"Jikina ya fara sakwarkwacewa" in ji Djokovic, bayan an fitar da shi daga Gasar US Open ta bana
Shugaban Hukumar Ƙwallon Ƙafar Nijeriya Musa Gusau ya yi murabus
Ɗanwasan Kamaru Carlos Baleba ya koma Man Utd daga Brighton
Habasha ta shiga takarar ɗaukar nauyin gasar AFCON ta 2028
An sayar da ƙwallon da Maradona ya ci Ingila da hannu a kan $3.35M
Ɗan Nijeriya Semi Ajayi ya taimaka wajen yi wa Man Utd dukan wulaƙanci a farkon Gasar Firimiya
Cristiano Ronaldo ya fara kakarsa ta 25 da ƙwallonsa na 977 a tarihin wasansa
EFCC ta fara binciken Hukumar kwallon kafa ta Nijeriya, NFF