| Hausa
AFIRKA
3 MINTI KARATU
Rasha ta zargi Amurka da tura ayyukan makamai masu yada cututtuka zuwa Afirka
Jami'in gwamnatin Rasha ya bayyana kasashe Afirka biyar da suka hada da Kamaru da Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango da Nijeriya da Saliyo da kuma Uganda da ake zargin Amurka da tura ayyukan makamai masu yada cututtuka.
Rasha ta zargi Amurka da tura ayyukan makamai masu yada cututtuka zuwa Afirka
Shugaban Rasha Vladimir Putin ya taba yin kira da a samar da hanyoyin hana yaduwar makamai masu guba a duniya. / Hoto: AA / AA

Rasha ta zargi Amurka da mayar da wani bangaren aikinta ''wanda ba a kammala shi ba'' na Ukraine kan binciken makamai masu yada cututtuka zuwa Afirka.

Ana kan gudanar da wannan aiki a kasashen Nijeriya da Kamaru da Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo da Saliyo da kuma Uganda, a cewar Igor Kirillov, shugaban sojin Rasha da ke kula da ayyukan binciken sinadarai da kare halittu, a yayin zantawarsa da manema labarai a birnin Moscow a ranar Talata.

"A yau, idan muka yi misali da Nijeriya, za mu ga cewa manufofin da aka bayyana na ayyukan da ake son aiwatarwa wajen inganta kiwon lafiyar al'umma ba su yi daidai da abin da yake a zahiri ba," in ji shi.

Jami’in na Rasha ya kara da cewa ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon ta yi ikirarin cewa ayyukan nazarin halittu a Nijeriya sun mayar da hankali a yaki da cutar kanjamau ta HIV/AIDS, kuma kashi 60 cikin 100 na masu fama da cutar a kasar, sun bi tsarin da aka ware na karbar maganin rage yaduwar cutar.

"Adadin masu cutar HIV bai sauya sosai ba a kasar, a halin da ake ciki yawan mutanen da ke dauke da cutar kusan daidai yake da na shekarar 2009, kazalika yawan mace-mace da ake samu a tsakanin masu dauke da cutar ya ragu," in ji Kirillov.

Jami'in ya nuna shakku kan manufar boye shaidun da za su iya bankado babban dan kwangilar Pentagon, kamar yadda bayanan cikin takardun kwagilar suka nuna.

"Takardu sun jaddada bukatar a takaita bincike a kan dan kwangilar, wato ( kwararrun Pentagon) kan su gudanar da gajerun tafiye-tafiye zuwa kasar Afghanistan da Iraki daga ofishinsu da ke birni Dubai idan har bukatar hakan ta taso," in ji shi.

Kirillov ya kara da cewa, "don kauce wa duk wasu zarge-zarge kan ma'aikatar tsaron Amurka Pentagon, sai aka aiwatar da ayyukan karkashin ma'aikatar harkokin wajen Amurka."

MAJIYA:TRT Afrika
Rumbun Labarai
Tiani: Dole ne Nijar ta warware matsalolin da suka daɗe suna dabaibaye ta kafin samun nasara
Majalisar Dattawan Aljeriya ta amince da buƙatar tura sojoji zuwa Nijar
Gabon ta janye takunkumin amfani da kafafen sada zumunta bayan watanni takwas
Kenya ta tabbatar da mutuwar mutum na biyu daga cutar Ebola
Ana fargabar mutane da dama suna ƙarƙashin ɓaraguzan gini mai hawa 12 da ya rushe a Kenya
Daga Nijeriya zuwa Kenya, mutane na tsawon rai amma ba tare da cikakkiyar lafiya ba
Hamshakiyar attajira ‘yar kasar Mali ta sa sarƙar zinare mai darajar dala miliyan 1.6
Ministocin makamashi na ƙasashen ECOWAS na taro kan ajiyar batura da dokokin kasuwannin lantarki
An saki wasu mata ’yan Turai biyu da aka yi garkuwa da su a Nijar bayan shafe watanni a tsare
Nijar: Hukumomi sun ɗauki matakan tsaro na gaggawa a Agadez bayan harin da ya kashe mutum 12
Kenya ta kulla yarjejeniyar $160m ta kiyaye muhalli, da goyon bayan magadan attajiran Amurka
Ghana na shirin tunkarar Ebola bayan ɓullar cutar a Kongo DRC da Kenya da Nijeriya
Kasashe da kungiyoyin kasa da kasa na taro a Geneva don habaka kokarin samar da zaman lafiya a Sudan
Darajar kuɗin Sudan ta faɗi, inda ake canza dala ɗaya an kan fam 10,000 na ƙasar
Uganda ta musanta samun  Ebola a ƙasarta bayan wata fasinja 'yar Nijeriya ta nuna alamun cutar
Gwamnatin Nijar ta haramta fitar da man fetur da gas zuwa ƙasashen waje
Ana hasashen kuɗin da Angola za ta kashe kan tallafin fetur a 2026 zai kai dala biliyan hudu
Shugaban Masar Al-Sisi ya ce zai sauka daga mulki a 2030 ba tare da tsawaita wa'adin mulkinsa ba
Africa CDC ta ce ba a san yadda aka kashe fiye da dala miliyan 700 na kuɗin yaƙi da Ebola ba
Ya zama dole Afirka ta daina tambayar ‘me duniya za ta sayar mana’ kawai