| Hausa
AFIRKA
3 MINTI KARATU
Rasha ta zargi Amurka da tura ayyukan makamai masu yada cututtuka zuwa Afirka
Jami'in gwamnatin Rasha ya bayyana kasashe Afirka biyar da suka hada da Kamaru da Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango da Nijeriya da Saliyo da kuma Uganda da ake zargin Amurka da tura ayyukan makamai masu yada cututtuka.
Rasha ta zargi Amurka da tura ayyukan makamai masu yada cututtuka zuwa Afirka
Shugaban Rasha Vladimir Putin ya taba yin kira da a samar da hanyoyin hana yaduwar makamai masu guba a duniya. / Hoto: AA / AA

Rasha ta zargi Amurka da mayar da wani bangaren aikinta ''wanda ba a kammala shi ba'' na Ukraine kan binciken makamai masu yada cututtuka zuwa Afirka.

Ana kan gudanar da wannan aiki a kasashen Nijeriya da Kamaru da Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo da Saliyo da kuma Uganda, a cewar Igor Kirillov, shugaban sojin Rasha da ke kula da ayyukan binciken sinadarai da kare halittu, a yayin zantawarsa da manema labarai a birnin Moscow a ranar Talata.

"A yau, idan muka yi misali da Nijeriya, za mu ga cewa manufofin da aka bayyana na ayyukan da ake son aiwatarwa wajen inganta kiwon lafiyar al'umma ba su yi daidai da abin da yake a zahiri ba," in ji shi.

Jami’in na Rasha ya kara da cewa ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon ta yi ikirarin cewa ayyukan nazarin halittu a Nijeriya sun mayar da hankali a yaki da cutar kanjamau ta HIV/AIDS, kuma kashi 60 cikin 100 na masu fama da cutar a kasar, sun bi tsarin da aka ware na karbar maganin rage yaduwar cutar.

"Adadin masu cutar HIV bai sauya sosai ba a kasar, a halin da ake ciki yawan mutanen da ke dauke da cutar kusan daidai yake da na shekarar 2009, kazalika yawan mace-mace da ake samu a tsakanin masu dauke da cutar ya ragu," in ji Kirillov.

Jami'in ya nuna shakku kan manufar boye shaidun da za su iya bankado babban dan kwangilar Pentagon, kamar yadda bayanan cikin takardun kwagilar suka nuna.

"Takardu sun jaddada bukatar a takaita bincike a kan dan kwangilar, wato ( kwararrun Pentagon) kan su gudanar da gajerun tafiye-tafiye zuwa kasar Afghanistan da Iraki daga ofishinsu da ke birni Dubai idan har bukatar hakan ta taso," in ji shi.

Kirillov ya kara da cewa, "don kauce wa duk wasu zarge-zarge kan ma'aikatar tsaron Amurka Pentagon, sai aka aiwatar da ayyukan karkashin ma'aikatar harkokin wajen Amurka."

MAJIYA:TRT Afrika
Rumbun Labarai
Burhan na Sudan ya buƙaci a cire siyasa a rabon tallafin yaƙi da sauyin yanayi ga ƙasashe mara ƙarfi
Greenpeace ta gargaɗi Ghana kan barazanar shara sakamakon shigo da tsofaffin tufafi miliyan 1 a mako
Yadda El Niño ke sake haifar da ɓarkewar cutar Zazzaɓin Rift Valley a Gabashin Afirka
BAMEX 2026: An fara baje-kolin fasahar tsaro ta ƙasa da ƙasa a Mali
Kotu a DR Congo ta yanke wa sojoji 66 hukuncin kisa saboda 'ja da baya a fagen daga'
Kwale-kwale dauke da ‘yan ci-rani ya kife a kusa da Senegal, mutum 21 sun rasu, in ji hukumomi
An yanke wa jagoran ƙungiyar asiri a Kenya hukuncin ɗaurin shekara 200 kan kisan yara 190
MƊD ta yi gargaɗin cewa El Nino za ta iya raba mutum miliyan uku da gidajensu a Gabashin Afirka
Shugaban Nijar Tiani ya karɓi baƙuncin takwaransa na Mali Assimi Goita a Yamai
Farashin burodi ya ninka cikin mako ɗaya a Sudan sakamakon ƙarancin fetur da fulawa
Ethiopia da Sudan sun rufe ofisoshin jakadancin juna bayan zarge-zargen tsoma baki a yaƙin basasa
Shugaban Benin ya sauya manyan hafsoshin soji bayan kusan shekara ɗaya da yunƙurin juyin mulki
Dangote ya ƙaddamar da aikin wajen adana man fetur na dala biliyan 2.5 a Namibia
Afirka ta Kudu ta tuhumi mutum biyu saboda satar fiye da dala dubu 580 a gonar Shugaba Ramaphosa
Ghana ta ƙwato fiye da cedi biliyan 18 ta hanyar binciken kuɗi – Babbar mai binciken kuɗi
Sojojin Sudan sun ce sun dakile hare-haren RSF a yankin Kogin Nilu
Wakilan musamman na China za su ziyarci Afirka don tattaunawar zaman lafiyar yanki
Nijar ta karɓi tankokin dakon man fetur 53 daga Aljeriya domin rage matsalar karancin mai
Ayarin motocin sojin Aljeriya ya isa birnin Arlit na Nijar
Saudiyya ta dakatar da shiga kasar daga Kenya saboda Ebola