| Hausa
TURKIYYA
2 MINTI KARATU
Turkiyya ta kai samame kan kungiyar masu aikata laifuka ta Comanchero ta kama mutum 37
Kungiyar mai cibiya a Australiya karkashin jagorancin Hakan Ayik tana gudanar da ayyukanta a fadin duniya kamar safarar miyagun ƙwayoyi da fashi da makami da kisan kai.
Turkiyya ta kai samame kan kungiyar masu aikata laifuka ta Comanchero ta kama mutum 37
“Ba za mu yafe wa duk wani gungun masu aikata miyagun laifuka ba, masu safarar ƙwaya. Za mu tarwatsa su duk irin ƙarfinsu tare da gurfanar da su a gaban ƙuliya," in ji Ministan Ali Yerlikaya. Hoto: AA Archive / AA Archive

Turkiyya ta kai smaame kan wata ƙungiyar ƙasa da ƙasa ta masu aikata miyagun laifuka ta Comanchero, inda aka kama mutum 37 da ake zargi a Istanbul, a cewar Ministan Harkokin Cikin Gida na Turkiyya.

An tarwatsa ƙungiyar Comanchero, wacce ke da cibiya a Australia da Hakan Ayik (REIS) ke jagoranta, take kuma ayyukanta a faɗin duniya, a yayin samamen da aka kai a Istanbul, akamar yadda Ali Yerlikaya ya faɗa a ranar Alhamis.

Yerlikaya ya ƙara da cewa an kama mutum 37 da ake zargi a yayin samamen.

“Ba za mu yafe wa duk wani gungun masu aikata miyagun laifuka ba, masu safarar ƙwaya. Za mu tarwatsa su duk irin ƙarfinsu tare da gurfanar da su a gaban ƙuliya," in ji ministan.

Da yake ƙarin bayani a kan ƙungiyar, Yerlikaya ya bayyana cewa an kashe ainihin shugaban ƙungiyar miyagun laifukan a shekarar 2018.

Ƙungiyar ta ci gaba da munanan ayyukanta a fadin duniya ƙarƙashin jagorancin Mark Douglas Buddle, ciki har da safarar miyagun ƙayoyi da kisan kai da fashi da makai da satar mutane don karɓar kuɗin fansa.

A shekarar 2022 an kama Buddle a Arewacin Cyprus ta Jamhuriyar Turkiyya sannan aka mayar da shi Australiya.

Hakan Ayik da Duax Hohepa Ngakuru, biyu daga cikin mambobin ƙungiyar sun karɓi jagorancinta tare da ci gaba da aiwatar da munanan ayyukan.

MAJIYA:TRT World
Rumbun Labarai
Kamfanin Fergani na Turkiyya ya tura tauraron ɗan'adam na gwaji na 6 sararin samaniya
Turkiyya, Qatar da Pakistan da Indonesia za su sanya hannu kan yarjejeniyar masana'antar tsaro
Antalya ya karɓi masu yawon buɗe ido miliyan 14 daga ƙasashen waje duk da ƙalubalen duniya
Spain na shirin sayen jirgin horar da mayaka na Hurjet kirar Turkiyya guda 15: Shugaban TAI
Turkiyya ta haramta wa shafukan sada zumunta yi wa 'yan ƙasa da shekara 15 rijista
Yarjejeniyar tsaro ta Makka ba ta ba da izinin kai hari kan ƙasashe ba - Turkiyya
Turkiyya ta yi wa Nijeriya ta’aziyya kan hatsarin jirgin soji
Shelar Antalya da Turkiyya ke jagoranta ta haɗa ƙasashe 21 a haɗin kan lumana kan sararin samaniya
Emine Erdoğan ta jagoranci kiran matan shugabannin duniya na son MDD tai tsarin kare yara a intanet
Turkiyya za ta ci gaba da magana kan Falasɗinawa: Erdogan
Zauren kotu ya dace da masu aikata laifukan yaƙi ba zauren Majalisar Ɗinkin Duniya ba: Erdogan
Jami’an Sojin Ruwa 30 na Saudiyya sun kammala karɓar horo a kamfanin tsaron Turkiyya, Baykar
Yadda Turkiyya ke taimaka wa Iraƙi wajen isar da albarkatun manta zuwa kasuwannin ƙasa da ƙasa
An wallafa jawabin Shugaba Erdogan na UNGA-81 a matsayin littafi cikin harsuna uku
Shugaban Turkiyya Erdogan ya buƙaci haɗin ƙan Musulmai, ya soki nuna wariya
Emine Erdogan ta buƙaci a rabu da ‘al’adar jefar da kaya' a koma ga tsarin sabuntawa
Erdogan ya yi kira da a gyara MƊD, ya nemi a soke ikon kujerar na-ƙi
Abincin Afirka daga Turkiyya
Shugaba Erdogan na Turkiyya ya tafi New York taron Majalisar Dinkin Duniya
'Turkiyya za ta duba buƙatun Saudiyya ƙarƙashin yarjejeniyar Makkah yayin da Houthi ke kai hari'