| Hausa
AFIRKA
2 MINTI KARATU
Chadi ta sanar da janye jakadanta daga Isra'ila
Kasar Chadi ta sanar da yi wa jakadanta da ke Isra’ila kiranye sakamakon hare-haren da kasar ke kai wa Gaza.
Chadi ta sanar da janye jakadanta daga Isra'ila
Chadi ta yi Allah-wadai da rasa rayukan da ake yi a Gaza da kuma neman a tsagaita wuta. Hoto/Others / Photo: Getty Images / Getty Images

Kasar Chadi ta sanar da yi wa jakadanta da ke Isra’ila kiranye sakamakon hare-haren da kasar ke kai wa Gaza.

A wata sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Wajen Chadi ta fitar a ranar Lahadi, ta yi Allah-wadai da irin yadda ake samun asarar rayuka a Gaza tare da kira kan a tsagaita wuta. Haka kuma ta yanke shawarar yi wa jakadanta kiranye daga Isra’ila zuwa N’Djamena domin tattaunawa.

“Chadi na mayar da hankali sosai kuma ta damu kan abin da ke faruwa a Gabas ta Tsakiya, musamman tashe-tashen hankulan da ba a taba ganin irinsu ba a Zirin Gaza.

“Sakamakon wannan bala’in, Chadi ta yi Allah wadai da rasa rayukan farar hula da dama tare da neman a tsagaita wuta wanda zai kai ga mafita mai dorewa ga Falasdinu,” in ji sanarwar.

“Dangane da haka ne aka yanke hukuncin yin kiranye ga jakadan da ke Isra’ila domin tattaunawa,” kamar yadda sanarwar ta kara da cewa.

Da alama ce Chadi kasar Afirka ta farko da ta soma daukar irin wannan matakin daga nahiyar Afirka, duk da cewa tuni kasar Turkiyya ta dauki wannan matakin na yi wa jakadanta kirane.

Haka ma kasashen Bolivia da Chile da Colombia da ke Kudancin Amurka tuni suka dauki matakin yanke dangantaka da Isra’ilar sakamakon ci gaba da kisan da take yi wa Falasdinawa.

Zanga-zangar kin-jinin Isra’ilar na ci gaba da kankama a kasashe da dama ciki har da Amurka da kuma Birtaniya. Zuwa yanzu akalla Falasdiniwa 9,970 Isra’ila ta kashe a Gaza, daga ciki 4,800 yara ne kanana, sannan 2,550 mata ne.

MAJIYA:TRT Afrika da abokan hulda
Rumbun Labarai
Tiani: Dole ne Nijar ta warware matsalolin da suka daɗe suna dabaibaye ta kafin samun nasara
Majalisar Dattawan Aljeriya ta amince da buƙatar tura sojoji zuwa Nijar
Gabon ta janye takunkumin amfani da kafafen sada zumunta bayan watanni takwas
Kenya ta tabbatar da mutuwar mutum na biyu daga cutar Ebola
Ana fargabar mutane da dama suna ƙarƙashin ɓaraguzan gini mai hawa 12 da ya rushe a Kenya
Daga Nijeriya zuwa Kenya, mutane na tsawon rai amma ba tare da cikakkiyar lafiya ba
Hamshakiyar attajira ‘yar kasar Mali ta sa sarƙar zinare mai darajar dala miliyan 1.6
Ministocin makamashi na ƙasashen ECOWAS na taro kan ajiyar batura da dokokin kasuwannin lantarki
An saki wasu mata ’yan Turai biyu da aka yi garkuwa da su a Nijar bayan shafe watanni a tsare
Nijar: Hukumomi sun ɗauki matakan tsaro na gaggawa a Agadez bayan harin da ya kashe mutum 12
Kenya ta kulla yarjejeniyar $160m ta kiyaye muhalli, da goyon bayan magadan attajiran Amurka
Ghana na shirin tunkarar Ebola bayan ɓullar cutar a Kongo DRC da Kenya da Nijeriya
Kasashe da kungiyoyin kasa da kasa na taro a Geneva don habaka kokarin samar da zaman lafiya a Sudan
Darajar kuɗin Sudan ta faɗi, inda ake canza dala ɗaya an kan fam 10,000 na ƙasar
Uganda ta musanta samun  Ebola a ƙasarta bayan wata fasinja 'yar Nijeriya ta nuna alamun cutar
Gwamnatin Nijar ta haramta fitar da man fetur da gas zuwa ƙasashen waje
Ana hasashen kuɗin da Angola za ta kashe kan tallafin fetur a 2026 zai kai dala biliyan hudu
Shugaban Masar Al-Sisi ya ce zai sauka daga mulki a 2030 ba tare da tsawaita wa'adin mulkinsa ba
Africa CDC ta ce ba a san yadda aka kashe fiye da dala miliyan 700 na kuɗin yaƙi da Ebola ba
Ya zama dole Afirka ta daina tambayar ‘me duniya za ta sayar mana’ kawai