| Hausa
DUNIYA
2 MINTI KARATU
An samu karuwar masu kyamar Musulunci a Jamus
“Muna fuskantar matukar karuwar nuna wariya ga Musulmai a Jamus. Wannan wani lamari ne da ya kamata mu nuna damuwa a kai da kuma dauka da muhimmanci.”
An samu karuwar masu kyamar Musulunci a Jamus
Ana yawan samun matsalolin cin zarafin Musulmi a Jamus. Hoto/AA / Others

Hukumomi a Jamus ranar Litinin sun nuna damuwa kan yadda ake samun karuwar kin jinin Musulmai a kasar tun bayan soma yaki a Gaza a ranar 7 ga watan Oktoba.

"Ba a amince da duk wani hari da za a kai kan Musulmai ko addini a Jamus ba,” kamar yadda mai magana da yawun gwamnati Steffen Hebestreit ya bayyana a wani taron manema labarai a Berlin.

“Musulmai miliyan biyar da ke Jamus suna da duk wani ‘yanci na samun kariya...,” kamar yadda ya kara da cewa.

Kungiyar kawance wadda ke yaki da kin jinin Musulunci (CLAIM) a makon da ya gabata ta yi gargadi kan karuwar kyamar Musulmai a daidai lokacin da ake samun karuwar rikici tsakanin Isra’ila da Falasdinawa.

“Muna fuskantar matukar karuwar nuna wariya ga Musulmai a Jamus. Wannan wani lamari ne da ya kamata mu nuna damuwa a kai da kuma dauka da muhimmanci,” kamar yadda Rima Hanano, shugabar kungiyar ta bayyana.

Kungiyar ta CLAIM ta tara rahotanni 53 da aka samu na barazana ga Musulmai, da nuna wariya a makonni biyu da rabi da suka gabata, daga ciki har da hare-hare goma da aka kai kan masallatai.

Za a iya cewa akwai irin wadannan rahotanni da dama na kyamar Musulmai wadanda ba a bayar da rahotonsu ba, misali wadannan sun hada da maganganu da aka yi na kyamar Musulmai a shafukan sada zumunta.

Kungiyar ta CLAIM ta yi kira kan a dauki matakai masu tsauri wadanda za a yi amfani da su domin yaki da kin jinin Musulunci da kuma bayar da kariya ga wadanda lamarin ya shafa.

MAJIYA:AA
Rumbun Labarai
Trump ya ce Qatar ta yi tayin ba shi kyautar jirgin sama samfurin 747 bayan ya nemi a ba shi aro
Gwamnatin Trump na binciken Ilhan Omar, za ta ƙwace takardarta ta ‘yar ƙasa tare da korar ta: Rahoto
An cire wani sashe na huhun Fafaroma Leo bayan yi masa tiyatar kansa - Fadar Batikan
Koriya ta Arewa ta 'harba makamai masu linzami da dama cikin tekun Japan'
Trump ya ce rashin ba shi kyautar Nobel ta Zaman Lafiya 'abin kunya ne'
Faransa ta ce za ta bai wa Saudiyya kariya a ɓangaren man fetur ɗinta
HRW: Tasa ƙeyar ’yan Ci-rani zuwa Afirka da Amurka ke yi azabtarwa ce
Trump na shirin kai wa Iran hari kafin zaɓen tsakiyar wa'adi a Amurka - rahoto
WHO ta yi kira ga Rasha da ta yi gaskiya game da rahotannin mutuwa sakamakon annobar ciwon huhu
Amurka ta janye dukka jiragen yaƙinta na B-1 daga sansanin sojin saman Birtaniya saboda tsoron hari
Trump ya yi gargaɗin cewa yaƙi da Iran zai zo ƙarshe ko ta halin ƙaƙa 'nan ba da jimawa ba’
An ceto baƙin-haure 260 a gaɓar tekun Mauritania
Sau takwas sojojin Amurka na yunƙurin kashe kansu a cikin USS Abraham Lincoln, in ji gwamnatin Trump
Kwamitin Zaman Lafiya na Duniya zai gabatar da shirin farfado da Gaza na dala biliyan $2.45: Rahoto
Erdogan a UNGA: Gaza ce sansanin tsare mutane mafi muni da rashin tausayi da abin kunya a zamaninmu
Trump ya yi wa Iran barazana, ya kira ICC ‘marar gaskiya‘, ya sauya sunan AI zuwa ‘SI’
Amurka ta kai 'yan ci-rani fiye da 25,000 da ta kora zuwa ƙasashen da ba su da alaƙa da su: Bincike
Antonio Guterres ya nemi a bai wa Afirka kujerun dindindin a Kwamitin Tsaro na MDD
Trump ya sa hannu kan sabuwar dokar takunkumi ga Rasha: China da India na iya fuskantar sabon haraji
Kasashen Yamma na shirin yaƙi da Rasha: Lavrov