| Hausa
AFIRKA
4 MINTI KARATU
Sojojin Nijeriya sun kashe ’yan bindiga 113, sun kama mutum 300 – Hedkwatar Tsaron Kasar
Manjo Janar Edward Buba ya ce dakarun kasar na rundunar Operation Hadin Kai sun kama kayayyakin Boko Haram da na Kungiyar ISWAP a Kukawa da Damboa da Monguno da Konduga a jihar Borno da ke Arewa maso gabashin kasar.
Sojojin Nijeriya sun kashe ’yan bindiga 113, sun kama mutum 300 – Hedkwatar Tsaron Kasar
Mai magana da yawun rundunar ya ce sun kashe mayakan Boko Haram da kungiyar ISWAP 17, sun kama 16 kuma sun ceto mutum shida da aka yi garkuwa da su da kuma kama albarusai iri daban-daban yayin farmakin da suka kai:Hoto/Nigerian Defence Headquaters / Others

Hedkwatar Tsaro ta Nijeriya (DHQ) ta ce dakarun kasar sun kashe ’yan kungiyar Boko Haram/ISWAP da sauran 'yan bindiga 113 kuma sun kama mutum 300 bayan wasu jerin farmaki da suka kai bangarori dama na kasar a cikin mako daya.

Daraktan Yada Labaran HedIkwatar Tsaron Manjo Janar Edward Buba ne ya bayyana haka lokacin da ya gana da manema labarai kan aikace-aikacen rundunar sojin kasar a Abuja ranar Alhamis.

Har ila yau ya ce dakarun sun kama masu satar man fetur 25 kuma sun kubutar da mutum 91 da aka sace. Kazalika ya ce sun gano makamai 129 da albarusai 717.

Ya ce dakarun kasar na rundunar Operation Hadin Kai sun kama kayayyakin Boko Haram da na Kungiyar ISWAP a Kananan Hukumomin Kukawa da Damboa da Monguno da Konduga a jihar Borno da ke arewa maso gabashin kasar.

Mai magana da yawun rundunar ya ce sun kashe mayakan Boko Haram da kungiyar ISWAP 17, sun kama 16 kuma sun ceto mutum shida da aka yi garkuwa da su da kuma kama albarusai iri daban-daban yayin farmakin da suka kai.

Ya ci gaba da cewa rundunar Operation Hadin Kai a ranar 2 ga watan Nuwamba, ta kawar da masu tayar da kayar baya da dama da kuma lalata kayayyakinsu a yankin Degbewa.

Manjo Janar Buba ya ce a shiyyar tsakiyar kasar, rundunar Safe Haven ta gudanar da wasu ayyuka a wani bangare na jihohin Kaduna da Filato, inda ta kashe ’yan bindiga biyar ta kama 14 kuma ta kubutar da mutum 15 da aka yi garkuwa da su.

A cewarsa, Rundunar Whirl Stroke ta gudanar da wani farmaki a wani wuri da ake zargin maboyar miyagun mutane ne a wasu bangarorin jihohin Nasarawa da Benue da kuma Filato, inda aka kawar da ’yan bindiga biyu, aka kama 10 kuma aka kubutar da mutum uku da aka yi garkuwa da su.

A arewa maso yamma, dakarun rundunar Hadarin Daji sun kawar da ’yan bindiga 30, da kama wasu bakwai tare da kubutar da mutum 31 da aka yi garkuwa da su a Katsina da Kebbi da kuma Zamfara yayin farmakin, a cewarsa.

Ya ce dakarun kasar sun gano bindigogi kirar AK47 guda 15 da bindiga samfurin RPG Tube da bam guda biyar da gurneti shida da kakin soji biyar da sauransu.

Haka dai mai magana da yawun hedkwatar tsaron kasar ya yi zayyana nasarorin da dakarun sojin kasar suka samu yayin ganawa da manema labaran.

MAJIYA:TRT Afrika
Rumbun Labarai
Tiani: Dole ne Nijar ta warware matsalolin da suka daɗe suna dabaibaye ta kafin samun nasara
Majalisar Dattawan Aljeriya ta amince da buƙatar tura sojoji zuwa Nijar
Gabon ta janye takunkumin amfani da kafafen sada zumunta bayan watanni takwas
Kenya ta tabbatar da mutuwar mutum na biyu daga cutar Ebola
Ana fargabar mutane da dama suna ƙarƙashin ɓaraguzan gini mai hawa 12 da ya rushe a Kenya
Daga Nijeriya zuwa Kenya, mutane na tsawon rai amma ba tare da cikakkiyar lafiya ba
Hamshakiyar attajira ‘yar kasar Mali ta sa sarƙar zinare mai darajar dala miliyan 1.6
Ministocin makamashi na ƙasashen ECOWAS na taro kan ajiyar batura da dokokin kasuwannin lantarki
An saki wasu mata ’yan Turai biyu da aka yi garkuwa da su a Nijar bayan shafe watanni a tsare
Nijar: Hukumomi sun ɗauki matakan tsaro na gaggawa a Agadez bayan harin da ya kashe mutum 12
Kenya ta kulla yarjejeniyar $160m ta kiyaye muhalli, da goyon bayan magadan attajiran Amurka
Ghana na shirin tunkarar Ebola bayan ɓullar cutar a Kongo DRC da Kenya da Nijeriya
Kasashe da kungiyoyin kasa da kasa na taro a Geneva don habaka kokarin samar da zaman lafiya a Sudan
Darajar kuɗin Sudan ta faɗi, inda ake canza dala ɗaya an kan fam 10,000 na ƙasar
Uganda ta musanta samun  Ebola a ƙasarta bayan wata fasinja 'yar Nijeriya ta nuna alamun cutar
Gwamnatin Nijar ta haramta fitar da man fetur da gas zuwa ƙasashen waje
Ana hasashen kuɗin da Angola za ta kashe kan tallafin fetur a 2026 zai kai dala biliyan hudu
Shugaban Masar Al-Sisi ya ce zai sauka daga mulki a 2030 ba tare da tsawaita wa'adin mulkinsa ba
Africa CDC ta ce ba a san yadda aka kashe fiye da dala miliyan 700 na kuɗin yaƙi da Ebola ba
Ya zama dole Afirka ta daina tambayar ‘me duniya za ta sayar mana’ kawai