| Hausa
TATTALIN ARZIKI
3 MINTI KARATU
Nijeriya da Saudiyya sun rattaba hannu kan yarjejeniyar mai da iskar gas
Ana sa ran yarjejeniyar za ta taimaka wajen habaka dangantaka tsakanin kasashen biyu, ta hanyar musayar bayanai da fasahohin da za su inganta hanyoyin cin moriyar juna.
Nijeriya da Saudiyya sun rattaba hannu kan yarjejeniyar mai da iskar gas
Karamin Ministan Albarkatun Man Fetur na Nijeriya, ya ce yarjejeniyar da aka kulla za ta samar da hadin gwiwa da kuma inganta mu’amalar fasaha tsakanin kasashen biyu. Hoto: Gwamnatin Nijeriya / Others

Gwamnatin tarayyar Nijeriya ta rattaba hannu kan wata yarjejeniyar fahimtar juna da ƙasar Saudiyya domin kafa tsarin hadin gwiwa tsakanin ƙasashen biyu a fannin mai da kuma iskar gas.

Ana sa ran yarjejeniyar za ta taimaka wajen haɓaka dangantaka tsakanin kasashen biyu ta hanyar musayar bayanai da fasahohi da za su inganta hanyoyin cin moriyar juna.

Gwamnatin Nijeriya, wacce ta samu wakilcin karamin Ministan Albarkatun Man Fetur na kasar Sanata Heineken Lokpobiri, tare da gwamnatin Saudiyya karkashin jagorancin Ministan Makamashinta Yarima Abdulaziz bin Salman, sun rattaba hannu kan yarjejeniyar a yayin babban taron kasar da kasashen Afirka kan tattalin arziki da ke gudana a birnin Riyadh.

Tun da fari a wata sanarwa da Ministan ya fitar ranar Alhamis ya ce yarjejeniyar za ta kawo ci gaba sosai wajen ƙarfafa alaƙar da ke tsakanin ƙasashen biyu tare da inganta hanyoyin da za a ci moriyar juna.

“Fa'ida ta farko da ake sa rai daga wannan yarjejeniya mai muhimmanci ita ce sauƙaƙa musayar fasaha,'' in ji sanarwar.

“Duba da ci gaban Saudiya a fannin fasahar haƙo mai da iskar gas, Nijeriya za ta samu ci gaba sosai daga musayar ilimi a wannan fannin da kuma ƙara yawan albarkatun man kasar,'' a cewar Ministan.

Karanta wani labarin mai alaƙa: Saudiyya za ta ƙulla yarjejeniyar dala miliyan 500 da ƙasashen Afirka

Yarima Abdulaziz bin Salman, wanda ya sanya hannu a madadin Masarautar Saudiyya, ya bayyana kyakkyawan fata game da tasirin da yarjejeniyar haɗin gwiwar za ta haifar wajen inganta fannin makamashin ƙasashen biyu.

Kazalika Yariman ya sanya hannu kan wasu yarjejeniyoyi da ƙasashen Afirka ciki har da Nijeriya da Senegal da Chadi da kuma Habasha don haɗin kai a abubuwan da suka shafi makamashi.

MAJIYA:TRT Afrika
Rumbun Labarai
Kotun Kenya ta ce a dakatar da aikin Matatar Mai ta Dangote ta dala biliyan 16
Dangote na shirin zuba jarin $10bn don shawo kan matsalar wutar lantarki a Nijeriya
Amurka ta ƙulla yarjejeniyar $414m kan aikin haƙar uranium a Nijar
Matatar Dangote ta sayar da hannayen-jarin fiye da naira biliyan 10 mintuna kaɗan bayan ƙaddamarwa
Matatar Dangote za ta buɗe sayar da hannayen-jari na Naira tiriliyan 2.15
Apple ya gabatar da iPhone Duo, wayarsa ta farko da ake rufewa
Aliko Dangote ya ƙaddamar da fara sayar da hannun-jarin matatar mansa ga jama'a
Uganda ta sanar da samun raguwar kaso 15% a hada-hadar fitar da kofi zuwa ƙasashen waje
Zuba jari a ɓangaren makamashi na Nijeriya na iya ƙaruwa cikin shekaru biyar – Hukumar IEA
Matatar Dangote ta Nijeriya za ta fara sayar da hannayen jari a karon farko nan da ‘yan kwanaki
Shirin bankin da ba ya karɓar ruwa ba don tallata wani addini ba ne – Gwamnan Babban Bankin Ghana
Trump ya soki Canada kan haraji cikin rigimar cinikayyar da Amurka ke yi da ƙasar
Kayan da Turkiyya ta fitar zuwa Afirka a 2026 sun haura na dala biliyan 13
Kuɗin Ghana ya koma fuskantar matsi, na Uganda na farfaɗowa, na Nijeriya zai iya sauyawa kaɗan
Amurka ta yi barazanar saka wa tattalin arzikin Iran takunkumin da 'duniya ba ta taɓa gani ba'
Gwamnatin Nijeriya za ta farfado da burtalan kiwo 417 a faɗin ƙasar
Za a gyara kamfanin NNPC tare da sayar da hannayen jarinsa a kasuwar hannayen jarin Nijeriya —Tinubu
Matatar Dangote ta fitar da tan fiye da 400,000 na man jiragen sama zuwa Turai a watan Yuli - Rahoto
Hukumar Kasuwanci Marar Shinge ta Afirka ta sanya hannu da wani kamfanin Nijeriya don inganta fito
A lokacin da cututtuka suka tsallaka iyaka: Manoman Afirka na neman sabbin matakan kariya