| Hausa
DUNIYA
9 MINTI KARATU
Kungiyar Hamas ta lalata motoci 160 na sojojin Isra'ila
Wannan shafi ya kawo muku sabbin bayanai a ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamba, kan hare-haren da Isra'ila ke kai wa Gaza bayan Hamas ta kutsa kai Isra'ila inda ta kai mata hare-haren ba-zata a ranar 7 ga watan Oktoba.
Kungiyar Hamas ta lalata motoci 160 na sojojin Isra'ila
Rundunar sojin Isra'ila ta ce an kashe dakarunta 43 tun da ta kaddamar da kutse ta kasa a Gaza. / Hoto: Reuters / Reuters

1900 GMT —Kungiyar Hamas ta lalata motoci 160 na sojojin Isra'ila

Sashen soji na kungiyar Hamas ya ce ya lalata motoci 160 na dakarun Isra'ila tun lokacin da suka kaddamar da hare-hare ta kasa a Gaza, yana mai cewa ya lalata motoci 25 a cikin kwana biyu da suka gabata.

Hakan na faruwa ne a yayin da rundunar sojin Isra'ila ta ce an kashe dakarunta 43 tun da ta kaddamar da kutse ta kasa a Gaza.

1830 GMT — Isra'ila ta kai jerin hare-hare ta sama a yankuna daban-daban na Gaza

Dakarun Isra'ila sun kaddamar da jerin hare-hare ta sama a yankuna daban-daban na Gaza, a cewar Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida da Tsaron Kasa ta Gaza.

Ma'aikatar ta fitar da sanarwa da ke bayani dalla-dalla kan jerin hare-hare ta sama da dakarun Isra'ila suka kai a sassa daban-daban na Gaza.

"Jiragen sama na dakarun mamaya sun kaddamar da jerin hare-hare a harabar Mahadar Saraya da ke Birnin Gaza,” in ji ma'aikatar, tana mai karawa da cewa Isra'ila ta kuma “kaddamar da samame a yankin Tal al Zaatar da kuma Asibitin Indonesian Hospital da ke arewacin Gaza."

Ta kara da cewa jiragen yakin Isra'ila sun kai hare-hare a arewaci da tsakiyar Birnin Gaza da yankin Al Nasr da kuma yankunan kusa da garin Jabalia da ke arewacin Gaza.

1610 GMT— Ma'aikatar Lafiya a Gaza na kokawa kan katse intanet

Ma’aikatar lafiya a Gaza ta ce ba za ta iya kirga adadin mutanen da Isra’ila ke kashewa a halin yanzu ba sakamakon katsewar hanyoyin sadarwa da intanet.

Wannan na zuwa ne bayan zargin da ake yi wa Isra’ila na kaddamar da yaki kan asibitoci a Gaza.

1443 GMT — 'Yan adawa a Faransa na caccakar Macron kan Gaza

Daya daga cikin ‘yan adawa a Faransa Mathilde Panot a ranar Asabar ta caccaki Shugaba Macron inda ta ce Macron din ya ki magana kan a daina kisa a Gaza sai da aka kashe “mutum 10,000.”

Wannan na zuwa ne kwana guda bayan Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bukaci Isra’ila da ta daina kisan jarirai da mata a Gaza.

Isra’ilar dai na ci gaba da kai hare-hare ba kakkautawa a Gaza inda take kashe daruruwan jama’a a kullum akasari yara kanana.

1020 GMT — Isra'ila ta daure malamin makaranta kan zargin sojojin kasar da aikata 'fyade'

Isra’ila a ranar Asabar ta dakatar da kuma tsare wani malamin makaranta kan sukar dakarun Isra’ila kan harin da suke kai wa farar hula da cin zarafin matan Falasdinawa inda malamin ya kira su da “masu kisan yara.”

“An tsare tare da dakatar da wani malamin makaranta daga aikinsa kan zargin sojojin Isra’ila da yi wa matan Falasdinawa fyade da kuma halasta harin da Hamas ta kai a ranar 7 ga watan Oktoba,” in ji wata sanarwa da sojin Isra’ila suka fitar.

A sakon da malamin tarihin ya wallafa a shafukan sada zumunta, ya ce tun shekarar 1948 sojojin Isra’ila ke yi wa mata fyade, sai dai ba a rubuta hakan a littattafai.

0850 — Asibiti mafi girma a Gaza Al-Shifa ya daina aiki

Jarirai akalla 39 na fuskantar barazanar mutuwa sakamakon karancin iskar oksijin a yayin da Asibitin Al-Shifa mafi girma a Gaza ya daina aiki ranar Asabar sakamakon luguden wuta da Isra'ila ke yi masa ta kowanne bangare, a cewar Ma'aikatar Lafiya ta Falasdinu.

Kazalika Ministan Lafiya na Falasdinu ya ce asibiti 20 cikin 35 sun daina aiki sakamakon bama-baman da Isra'ila ke harba musu.

0820 — Za a binne gawawwakin mutum 100 a kabari daya a harabar Asibitin Al-Shifa da ke Gaza

Ma'aikatar Kiwon Lafiya ta Falasdinu ta ce za a haka babban kabari a cikin harabar Asibitin Al-Shifa ranar Asabar sannan a binne gawawwakin mutum 100 da ke yashe a asibitin.

Da yake tattaunawa da gidan talbijin na Al Jazeera da safiyar Asabar, Darakta Janar na Ma'aikatar Dr. Munir Al-Borsh ya ce Isra'ila ta kwashe dare na uku a jere tana luguden wuta a kusa da asibitin.

“Ana yin ruwan bama-bamai kusan kowane minti daya, da nufin samun hanyar shiga asibitin,” in ji shi, inda ya kara da cewa hare-haren Isra'ila sun hana motocin daukar marasa lafiya samun damar shiga ko fita daga asibitin.

“An yi mana kawanya a harabar Asibitin Al-Shifa,” a cewarsa.

A nata bangaren, kungiyar likitoci ta Doctors Without Borders (MSF) ta wallafa sako a shafin X cewa: "A sa'o'i kadan da suka gabata, ana ta kai hari babu kakkautawa a Asibitin Al-Shifa."

0750 — Lokacin surutu ya kare, ya kamata a dauki mataki kan rikicin Gaza - Raisi

Shugaban kasar Iran Ebrahim Raisi ranar Asabar ya ce lokacin surutu ya kare don haka yanzu lokacin daukar mataki ne a kan rikicin Gaza a yayin da yake kan hanyar tafiya Sudiyya domin halartar taron Kasashen Larabawa da na Musulmai.

"Batun Gaza ba na yin surutu ba. Ya kamata a dauki mataki," in ji Raisi a filin jirgin saman Tehran kafi ya tashi zuwa birnin Riyadh na Saudiyya, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya rawaito.

Ya kara da cewa: "A yau, hadin kan kasashen Musulmai yana da matukar muhimmanci."

0700 — Isra'ila tana harba bama-bamai da kashe 'jarirai da mata da tsofaffi' a Gaza — Shugaban Faransa Macron

Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya yi kira ga Isra'ila ta daina harba bama-bamai kan fararen-hula a Gaza, yana mai cewa babu wata hujja ta yin haka.

A hira da BBC, Macron ya ce Isra'ila tana da ikon kare kanta bayan harin da Hamas ta kai mata ranar 7 ga watan Oktoba, sai dai ya kara da cewa: "Ana harba bama-bamai da kashe wadannan jarirai da mata da tsofaffi. Babu wata hujja ta yin haka. Saboda haka muna kira ga Isra'ila ta daina."

0629 GMT — An zargi Isra'ila da 'kaddamar da yaki' a asibitocin Gaza masu cike da jama'a

Ana ci gaba da gumurzu a kusa da asibotocin Gaza masu cike da jama'a, inda jami'an Falasdinu suka ce Isra'ila tana jefa musu abubuwan fashewa da yin luguden wuta.

"Yanzu haka Isra'ila ta kaddamar da yaki a asibitocin Gaza," a cewar Mohammad Abu Selmeyah, daraktan Asibitin Al Shifa.

Daga bisani ya ce Isra'ila ta kashe mutum akalla 25 a makarantar Al-Buraq da ke Birnin Gaza, inda mutanen da ta rusa wa gidaje suke samun mafaka.

Jami'ai a Gaza sun ce Isra'ila ta harba rokoki a harabar Asibitin Al Shifa, wanda shi ne mafi girma a yankin, da safiyar Juma'a, sannan ta lalata Asibitin Indonesia kuma an cinna wuta a cibiyar kula da masu ciwon kansa ta Asibitin Nasser Rantissi.

MAJIYA:AA, AFP, Reuters, TRT World