| Hausa
TATTALIN ARZIKI
3 MINTI KARATU
'NNPC ya gaza biyan kudin mallakar wani bangare na matatar mai ta Dangote'
Kamfanin Mai na Kasa na Nijeriya (NNPC) ya dugunzuma game da bukatarsa na kaiwa matatar mai ta Dangote danyen mai na dala biliyan daya, a matsayin kudin mallakar kaso 20 na matatar, in ji BusinessDay.
'NNPC ya gaza biyan kudin mallakar wani bangare na matatar mai ta Dangote'
Shugaban kamfanin mai na Nijeriya (NNPC) Mele Kiyari, ya ce za a cigaba da neman mai a kasar don bunkasa tattalin arziki / Others

Kamfanin mai na Nijeriya NNPC na neman hanyoyin da zai dinga bayar da danyen man ga masu sarrafa shi a cikin gida, wadanda a yanzu suke ƙorafin wannan mataki zai iya jefa samuwar masu zuba jari cikin hatsari a bangaren sarrafawa da sayar da albarkatun man.

Tun bayan kaddamar da matatar mai ta Dangote da za ta dinga tace mai ganga 650,000 a kowacce rana a watan Mayu, ta zama kamar kango, tana jiran a kai mata ɗanyen mai, kuma dole a yanzu NNPC ya cika yarjejeniyar da aka kulla ko ya rasa mallakar kaso 20 na matatar.

Majiyoyi a Ma'aikatar Albarkatun Man Fetur da ke Abuja na cewa Nijeriya na fuskantar hatsarin gaza mallakar kaso ashirin na matatar Dangote, saboda gaza cika ka'idojin yarjejeniyar da aka kulla na mallakar wani bangare na matatar.

A karon farko, jaridar intanet ta BusinessDay ta yi kokarin rawaito cewa kason gwamnati a matatar ya kai dala biliyan 2.7, kuma an shirya gwamnatin tarayya za ta biya don mallakar kaso 20.

An amince da tsarin biyan kudaden, za a biya tsabar kudi da kuma kai wa matatar man ɗanyen mai.

NNPC ya ɓoye bayanai game da tsarin biyan kudaden, kuma bai taba bayyana wa 'yan Nijeriya yadda abun yake ba.

Baya ga biyan dala biliyan daya, an kuma amince NNPC zai kaiwa matatar Dangote danyen mai na dala biliyan daya, sannan zai biya sauran dala miliyan 700 daga ribar da zai samu daga matatar man.

A farkon watan nan an rawaito cewa kamfanin man zai kai wa matatar Dangote danyen mai a manyan jiragen ruwa da za a yi amfani da shi a matsayin gwaji a watan Disamba.

A jawabin da Dangote ya yi yayin kaddamar da matatar man a watan Mayu, ya bayyana cewa za ta biya bukatar mai ga Nijeriya da kasuwannin Afirka.

MAJIYA:TRT Afrika da abokan hulda
Rumbun Labarai
Kotun Kenya ta ce a dakatar da aikin Matatar Mai ta Dangote ta dala biliyan 16
Dangote na shirin zuba jarin $10bn don shawo kan matsalar wutar lantarki a Nijeriya
Amurka ta ƙulla yarjejeniyar $414m kan aikin haƙar uranium a Nijar
Matatar Dangote ta sayar da hannayen-jarin fiye da naira biliyan 10 mintuna kaɗan bayan ƙaddamarwa
Matatar Dangote za ta buɗe sayar da hannayen-jari na Naira tiriliyan 2.15
Apple ya gabatar da iPhone Duo, wayarsa ta farko da ake rufewa
Aliko Dangote ya ƙaddamar da fara sayar da hannun-jarin matatar mansa ga jama'a
Uganda ta sanar da samun raguwar kaso 15% a hada-hadar fitar da kofi zuwa ƙasashen waje
Zuba jari a ɓangaren makamashi na Nijeriya na iya ƙaruwa cikin shekaru biyar – Hukumar IEA
Matatar Dangote ta Nijeriya za ta fara sayar da hannayen jari a karon farko nan da ‘yan kwanaki
Shirin bankin da ba ya karɓar ruwa ba don tallata wani addini ba ne – Gwamnan Babban Bankin Ghana
Trump ya soki Canada kan haraji cikin rigimar cinikayyar da Amurka ke yi da ƙasar
Kayan da Turkiyya ta fitar zuwa Afirka a 2026 sun haura na dala biliyan 13
Kuɗin Ghana ya koma fuskantar matsi, na Uganda na farfaɗowa, na Nijeriya zai iya sauyawa kaɗan
Amurka ta yi barazanar saka wa tattalin arzikin Iran takunkumin da 'duniya ba ta taɓa gani ba'
Gwamnatin Nijeriya za ta farfado da burtalan kiwo 417 a faɗin ƙasar
Za a gyara kamfanin NNPC tare da sayar da hannayen jarinsa a kasuwar hannayen jarin Nijeriya —Tinubu
Matatar Dangote ta fitar da tan fiye da 400,000 na man jiragen sama zuwa Turai a watan Yuli - Rahoto
Hukumar Kasuwanci Marar Shinge ta Afirka ta sanya hannu da wani kamfanin Nijeriya don inganta fito
A lokacin da cututtuka suka tsallaka iyaka: Manoman Afirka na neman sabbin matakan kariya