| Hausa
AFIRKA
2 MINTI KARATU
Gwamnatin soji ta Gabon ta sanar da ranar zabe a kasar
Majalisar mulkin Gabon ta sanar da cewa za a gudanar da zabe a kasar a watan Agustan shekarar 2025 bayan juyin mulkin da aka yi wa Shugaba Ali Bongo Ondimba.
Gwamnatin soji ta Gabon ta sanar da ranar zabe a kasar
Gwamnatin riƙon ƙwarya ta kuma sanar da cewa za a gabatar da daftarin kundin tsarin mulki a karshen watan Oktoba na shekarar 2024,/  Hoto: Reuters / Others

Shugabannin sojojin kasar Gabon, wadanda suka hambarar da Shugaba Ali Bongo Ondimba a watan Agusta, sun sanar da cewa za a gudanar da zabe a watan Agustan shekarar 2025 a ƙarƙashin wani jadawalin da zai fara hasashen tattaunawar kasa.

"Agustan 2025: zaɓe da kuma kawo ƙarshen miƙa mulki," kamar yadda mai magana da yawun gwamnatin ya faɗa a gidan talabijin na ƙasar a ranar Litinin.

Za a gabatar da wa'adin lokacin ga wani taron ƙasa wanda ya ƙunshi dukkan "muhimman masu ruwa da tsaki" na kasar, wanda aka tsara yin sa a watan Afrilun 2024

Gwamnatin riƙon ƙwarya ta kuma sanar da cewa za a gabatar da daftarin kundin tsarin mulki a karshen watan Oktoba na shekarar 2024, kuma za a gudanar da zaben raba gardama kan amincewa da shi a tsakanin Nuwamba zuwa Disamba 2024.

MAJIYA:TRT Afrika da abokan hulda
Rumbun Labarai
Ziyarar Afirka: Fiye da mutum 500,000 ake sa ran sun halarci taron ibada na Fafaroma Leo a Kamaru
Yara mata ne suka fi cutuwa daga yaƙin Sudan da aka manta da shi
Fafaroma Leo ya nufi Kamaru ƙasa ta biyu a ziyararsa ta Afirka
Yaƙi ya jefa fiye da kashi 70 cikin 100 na 'yan ƙasar Sudan cikin talauci, in ji MƊD
Yadda yakin Iran ke shafar tattalin arziki, yanki da siyasar Afirka
Za a cim ma yarjejeniyar bututun gas na Nijeriya-Maroko kan biliyan $25 a bana: Jami'i
Fafaroma Leo ya fara ziyararsa ta farko zuwa Afirka
Matsalar yunwa a Sudan: Miliyoyin mutane na cin abinci sau ɗaya a rana
Ana gudanar da zaɓen shugaban ƙasa a Jamhuriyar Benin
Shugaban ƙasar Djibouti Guelleh ya sake yin nasara karo na shida
Ana gudanar da zaɓen shugaban ƙasa a Djibouti inda Guelleh da ke mulki ke neman wa'adi na shida
Daga hanyoyin mulkin mallaka zuwa na korar mutane: Afirka da siyasar korar baƙi daga wata ƙasa
Yadda ajujuwan Afirka ke fuskantar jarrabawa mafi tsauri a duniya
Kamaru ta ce ‘yan kasarta 16 sun mutu yayin taya Rasha yaki da Ukraine
Dalilin da ya sa Kenya da Ethiopia suka zama manyan masana'antun furanni a duniya
Ambaliyar ruwa ta kashe mutane 15 a Angola
Senegal ta haramta wa jami'an gwamnati tafiye-tafiye marasa muhimmanci zuwa ƙasashen waje
Yadda aikin dala miliyan 240 ke bai wa al’umar gaɓar teku a Benin da Mauritania damar gwagwarmaya
Gwamnatin Madagascar ta daƙile yunƙurin kashe shugaban ƙasar Michael Randrianirina
Sudan ta yi Allah wadai da 'mummunan' harin da RSF ta kai wani asibiti yayin allurar rigakafin yara