Manyan kungiyoyin duniya irin su Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya sun gaza wurin shawo kan matsalolin duniya inda suka kara "ta'azzara" su, in ji Daraktan Watsa Labarai na Turkiyya.
A wata makala da ya rubuta a wata mujalla ta Sifaniya mai suna Atalayar a ranar Asabar, Fahrettim Altun ya bayyana cewa "a bayyane take cewa dole ne a kafa kungiyoyin kasa da kasa bisa la'akari da sabon karni da sabon zamani, tare da la'akari da yadda sabbin abubuwa ke daidaita."
A makalar mai taken "Turkiyyar Erdogan na samar da mafita a wuraren da Majalisar Dinkin Duniya ta gaza", Altun ya ce Ankara na shirin amfani da hanyoyi daban-daban wadanda suka zo daidai da tsarin Shugaba Recep Tayyip Erdogan yake yawan magana a kai na cewa, "Duniya ta fi biyar girma," inda yake nufin mambobin dindindin na Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya wadanda suka hada da Amurka da Birtaniya da Faransa da Rasha da China.
Domin magance matsalolin duniya da na yankuna, Turkiyya na amfani da hanyoyin jinkai da na diflomasiyya, in ji Fahrettin Altun.
"Sakamakon nasarorin da aka samu a 'yan shekarun nan, ana bai wa Turkiyya girma a matakin kasa da kasa inda kuma ta taka rawa wurin magance matsalolin yankuna musamman a Gabas ta Tsakiya da yankin Caucasus," in ji shi.
Kan batun rikicin Isra'ila da Falasdinu, ya bayyana cewa matsayar da take da shi mai tare da mafita karkashin jagorancin Shugaba Erdogan, wadda ta mayar da hankali kan ayyukan jinkai ta tabbatar da hakan.
Kamar yadda aka nuna a matsalolin da suka shafi Ukraine da Karabakh da yankuna, a daidai lokacin da Jamhuriyar Turkiyya ta shiga karni na biyu, kasar ta zama babbar jagora a yankin da take," in ji Altun.















